An Kubutar Da Wani Fasto Daga Hannun Boko Haram

0
331
Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA gidauniya mai zaman kanta da ake kira Kaltum Foundation da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu sun kubutar da wasu mutane biyu a hannun Boko Haram sun kuma mika su ga gwamnatin jihar Borno.
Wadannan mutane sun hada ne da limamin wata cocin Living Faith Church da ke a Maiduguri, Fasto Moses Oyeleke da wani dan’uwansa da aka yi garkuwa da su watanni bakwai da suka gabata, yayin da suke hanyar su zuwa garin Chibok, a dai dai lokacin da suka isa garin Bama kafin su shiga Chibok.
Fasto Moses Oyeleke da aka kubutar da shi a ranar Lahadi, ya ce har yanzu dan uwansa na nan a hannun mutanen da suka yi garkuwa da su. Fasto Moses yace ya yi matukar farin ciki da ya dawo gida. Sai dai ya kara da cewa babu wata azaba da aka gana masa yayin da yake hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Da yake zantawa da manema labarai  a Maiduguri, Fasto Moses Oyeleke ya ce masu garkuwa da shi sun nemi ya musulunta ya bar addininsa amma kuma ba tare da wata tsangwama ba, ya kuma ce sun yi zaman lafiya da shi a tsawon lokaci da ya kwashe a wurinsu.
Wata yarinya ‘yar shekaru 14 da kungiyoyi masu zaman kansu suka kubutar da ita bayan an sace ta a gidansu da ke wani kauye a cikin karamar hukumar Askira Wuba dake kudancin jihar Borno, mai suna Jagilaye Ibrahim, ta bayyana wa manema labarai  irin hali da fada a ciki a hannun ‘yan Boko Haram.
Jagilaye Ibrahim, tace ta kwashe watanni tara a hannun masu garkuwa da ita ta kuma ga ana tursasa wa wasu ‘yan mata da su ma ake garkuwa da su ana aurar da su, sai dai ta ce ba a yi mata irin wannan auren ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here