BADAKALAR FILI: Shugaban Kwalejin Fasaha Ta Kano Ya Musanta Zargin Da Ake Yi Masa

0
458

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABAN kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya musanta zargin da kungiyar malaman kwalejin ta ASUP da kungiyoyin dalibai suka yi na cefanar da wasu filaye mallakin makarantar.

Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya bayyana hakan ne, jim kadan bayan wata zanga-zangar lumana da ta wakana a harabar makarantar, a wani mataki na nuna fushinsu kan zargin da suke yi cewar gwamnatin Kano ta dau gabarin sayar da wani bangare na kwalejin, wanda hakan suka ce kai ya barazana da ci gaban harkar ilmin daliban.

An zargi shugabar makaranta da amsar kudin dalibai da kuma yunkurin cefanar da wasu filaye na makarantar. Rahotanni sun ruwaito cewa, Farfesa Kurawa ya kara da cewa, shakka babu gwamnatin Kano ko kadan ba ta dauki wannan mataki ba. A maimakon haka ta mayar da hankali ne wajen bunkasa sha’anin koyo da koyarwar dalibai.

Shugaban kwalejin ya kuma ba da tabbacin gabatar da koken kungiyar ASUP ga Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, don ganin an kare muradansu da suka shafi ci gaban dalibai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here