Tashar Talbijin Ta Al-Irshaad Garkuwar Al’umma Ce Baki Daya-Sheikh Jingir

  0
  484
  Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir,

   Isah Ahmed Daga Jos 

  A makon da ya gabata ne kungiyar yada addinin musuluncin nan ta  Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, ta gudanar da gagarumin taron kaddamar da tashar talbijin ta tauraron dan ‘adam da ta bude mai suna Al-Irshaad a babban birnin tarayya Abuja.

  Wakilinmu ya tattauna da shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, kan manufar kafa wannan tasha da abubuwan da ta kunsa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

   

  GTK: Mene ne makasun bude tashar gidan talabijin na Al-Irshaad da kungiyar Izala ta yi?

  Sheikh Jingir: Kowa ya san aikin wannan kungiya shi ne wa’azi da karantarwa. Kuma karantarwar nan ya kunshi makarantun firamare da sakandire da manyan makarantu. Kuma salon karantarwar nan bayan tsari na makaranta, akwai tsarin tarurrukan wa’azi.

  An sanmu da wa’azi a kauyuka da garuruwa da birane a dukkan jihohin kasar nan, har da kasashen waje.

  Yanzu Allah ya kawo mu zamanin da akwai rediyo da talbijin da jaridu da mujallu. Kuma dukkan wadannan hanyoyi ne na sadar da sako zuwa ga mutane a birane da kauyuka.

  Don haka manufar bude wannan tashar talbijin ta Al-Irshaad da wannan kungiya ta yi shi ne domin mu ci gaba da gudanar da wannan aiki da muka sanya a gaba na wa’azi da karantar da addinin musulunci, don mu dora bayin Allah kan shiriya, don  tsamo su daga bata.

  Shi ya sa muka sanya wa wannan tasha suna Al-Irshaad wato ma’ana shiriya daga Allah. Wato shiryar da mutane su bar bata, su dawo kan hanya ta gaskiya.

  Saboda haka za ka ga shirye-shiryen da wannan tashar take gabatarwa na karantar da Alkura’ani mai girma da Hadisan Manzon Allah SAW da litattafan Fikihu da maganganun aure da noma da  gado da sana’o’in hannu da hulda tsakanin al’umma da dai sauransu.

  A takaice wannan tasha shirye-shiryen da take gabatarwa, ya shafi rayuwar dan Adam baki daya. Don haka muka bude wannan tasha domin sakonmu ya shiga ko ina a duniya.

  Kuma idan ka dubi duniyar yau a harkokin yada labarai, za ka ga ko labari aka bayar cewa wani ya kai babansa Makkah ya saya masa gida. Ba su cika mayar da hankali kan irin wannan labarai ba. Sai labaran yake-yake da fadace-fadace. Amma ita wannan tasha tana mayar da hankali ne kan labaran alheri.

  GTK: Wato a takaice wannan tasha za ta zama kamar garkuwa ce ga al’umma?

  Sheikh Jingir: Kwarai da gaske ita wannan tasha garkuwa ce ga al’umma baki daya, musulmi da wanda ba musulmi ba. Domin ya zuwa yanzu mun sami masu rubuto mana fatan alheri da godiya daga al’ummar musulmi har da kiristoci sun ce mana suna samun tarbiyyar ‘ya’yansu da matansu da makwaftansu ta hanyar shirye- shiryen da wannan tasha take gabatarwa. Saboda haka wannan tasha garkuwa ce ga dukkan ga al’umma da musulmi da wanda ba musulmi ba.

  GTK: Wannan tasha tana watsa shirye- shiryenta ne a wani sashi na duniya, ko tana watsa shirye-shiryenta ga duniya ne baki daya?

  Sheikh Jingir: To wannan tasha tana watsa shirye-shiryenta ne ga duniya baki daya. Domin ka ga a wajen musulmi  cibiyar duniya ita ce Makkah. Ina tafiya a Makkah  bayan an sauko daga Arfa, a aikin hajjin da ya gabata,  sai wani mutum ya tsare ni ya ce ya san ni. Na ce aina ya san ni? Ya ce a talbijin yana ganin wa’azina a talbijin ya ce shi daga Ghana yake.

  Bayan ya wuce muka sake haduwa da wani ya ce shi ma daga Beljiyom yake shi ma yana ganin wa’azina a talbijin. Akwai mutane da dama daga kasashen Afrika da Turai da Asiya da suka rubuto mana cewa suna ganin shirye-shiryen da muke gabatarwa a kasashen da suke zaune. Don haka wannan tasha tana gabatar da shirye-shiryenta ne ga duniya gabaki daya.

  GTK: Mene ne babban burin wannan kungiya kan wannan tasha?

  Sheikh Jingir: Babban burinmu shi ne Allah ya ba mu ikon ci gaba da wannan aiki na wa’azantarwa da muka sanya a gaba.

  GTK: Ganin akwai tashoshi na gidajen talbijin da suke nuna shirye-shiryen da ba su dace da addininmu da al’adunmu ba, wanne kira za ka yi ga al’ummarmu kan irin wadannan tashoshi na Al-Irshaad da suke nuna shirye-shiryen addininmu?

  Sheikh Jingir: Yana daga cikin abin da nake gaya maka ka ga wanda Allah ya taimake shi, ya sanya wannan tashar talbijin gidansa, to, ya bude makaranta ta musamman a gidansa. Domin da shi da matansa da ‘yayansa da ‘yan uwansa da sauran makwatansa za su sami alherin wannan tasha. Domin ka ga wannan tasha daga cikin karantarwar da malamanmu suke yi akwai tarbiyantar da dan Adam da tarbiyyantar da yara da tarbiyyar zaman aure da dukkan abubuwan da suka shafi rayuwar dan Adam ta duniya da lahira.

  Don haka halin da ake ciki na tabarbarewar tarbiyya muna kira ga jama’a su yi kokari su kauce wa tashoshin gidajen talbijin da suke nuna wa iyalansu  batsa, domin su tsira a duniya da lahira..

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here