Yadda Kayyade Kudin Aurena N137,000 Ya Janyo Wa ‘Yan Mata Tsangwama

0
447

Rabo Haladu Daga Kaduna

A kauyen Kera, wata hudu ke nan rabon da a daura aure. Hakan dai ya biyo bayan wani tsari ne da basaraken garin ya bullo da shi da nufin saukaka wa samari wahalhalun aure—amma lamarin ya haifar da takaddama.

“Sun zo sun kafa mana wata doka ta iyayenmu ‘ya’yanmu bisa aure, sun ce wai ya yi kudi”, inji Malam Idi Gayya, wani magidanci a kauyen.

Ya kuma kara da cewa, “Sun sa mana kudin ‘yan matanmu N137,000, ba man shafawa, ba lefe, ba komai; mu kuma mun ce ba ma ra’ayin wannan”.

Malam Idi dai na cikin wadanda ke ganin kudin aure bai yi yawa ba don haka kayyade shi wani sabon abu ne da ba a taba ji ba kaka da kakanni.

Dagacin garin ya ce ya bullo da wannan tsari ne bayan ya tuntubi iyayen yaran.

“Da ma duk abin da za ka yi sai an samu mai so sai an samu mara so, in dai abin alheri ne”, inji shi.

Amma wata uwa ta kwatanta matakin da wulakantar da matan garin.

A cewarta, “Muna da ‘ya’ya mata an mai da su gwanjo. An kada masu [kararrawa] an hana samari su nema su yi masu abin duniya.

“Kudin aure an yanke N137,000 — kudin nan ne zai yi wa yara kayan kicin, ya yi masu kayan kwalliya, ya yi masu zannuwan da za su fita?”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here