Za Mu Kai Gwamnatin Oyo Kotu Kan Kafa Dokar Hana Kiwo-Bayari

  0
  524
  Alhaji Sale Bayari ,,

  Isah Ahmed Daga Jos 

  KWANAKIN baya ne gwamnatin jihar Oyo ta fara yunkurin kafa dokar hana kiwo a jihar, kamar yadda jihohin Benuwai da Taraba suka yi. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan, Alhaji Sale Bayari. Wanda ya je gaban majalisar dokokin  jihar, ya gabatar da kukan al’ummar Fulani kan wannan yunkuri. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: Kwanakin baya mun sami labarin cewa ka je gaban majalisar dokokin jihar Oyo, kan kokarin da gwamnatin jihar take yi na kafa dokar hana kiwo a jihar, mene ne ya kai ka majalisar?

  Bayari: To wannan dokar hana kiwo da ake son kafawa a jihar Oyo, ta zo mana da bazata kuma ta zo mana da mamaki. Don haka Lokacin da muka sami wannan labari, sai muka je muka sami tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo muka roke shi ya sa baki kan wannan yunkuri da ake yi, na kafa dokar hana kiwo a jihar Oyo.

  Domin idan aka kafa wannan doka, al’ummar Fulani za su shiga bala’i a jihar. Saboda duk Fulani makiyaya da suke jihohin yankin Yarbawa guda 6, kashi 50 bisa 100 suna jihar ne. Saboda yawan jihar da yawan wuraren kiwon da ake da su a jihar.

  Domin wannan jiha tun lokacin su marigayi Sardauna aka je aka kafa wuraren kiwo sama da fadin eka dubu 30. Ka ga wannan ya nuna cewa tun lokacin su Sardauna, an san muhimmancin kiwo a wannan jiha.

  Don haka muka roki tsohon shugaban kasar, muka ce ya hada mu da masu fada aji a jihar. Domin mu roki a dakatar da wannan yunkuri na hana kiwo a wannan jiha. Idan kuma ya zama dole a yi dokar,  to, a yi dokar yadda ta dace ta yadda al’ummar Fulani ba za su cutu ba.

  Don haka muka je gaban majalisar dokokin jihar muka gabatar da koke- kokenmu, kan yadda muka ga wannan doka. Saboda yadda muka ga wannan doka, ta yi niya ne ta kawar da dukkan wani Bafulatani makiyayi a wannan jiha, kamar yadda aka yi a jihar Benuwai.

  Wato ana son a labe da guzuma a harbi karsana ne. A ce an kafa wannan doka ne domin a sami zaman lafiya, tsakanin makiyaya da manoma. Idan zaman lafiya ake so tsakanin makiyaya da manoma, ai  ba fitar da makiyaya za a yi ba.

  Abin da ya kai mu gaban majalisar ke nan, muka kai kukanmu. Kan cewa wannan doka ba za mu amince da ita ba. Saboda a ce a wannan zamani kana da shanu 50, a ce ba za ka fita ka nemi ciyawar Allah, ka ciyar da su ba. Sai dai ka je ka yi hayar gona ko daji ka katange,  ka nemo ruwa ka nemo masu abincin da za su ci, nawa za ka kashe?. Don haka muka kai masu wannan kuka amma sun ki yarda.

  GTK: Ganin cewa gwamnatin jihar nan ta Oyo ba ta da niyar dakatar da wannan kuduri, a nan wane mataki ne kuke shirin dauka kan wannan al’amari?

  Bayari: To yanzu muna nan muna shawarwari kan wannan al’amari. Kuma idan ba a dauki mataki ba kan wannan al’amari, za a iya samun damuwa a wannan jiha, kamar yadda aka samu a jihar Benuwai. Domin yanzu da aka kafa wannan doka a jihar Benuwai, an tashi da kwance uwa kwance. Babu manomi babu makiyaya, mutane ne suna nan suna zaman gudun hijira ko’ina a jihar. Yanzu mutane da dama a jihar, ba sa iya zuwa garuruwa da kauyukansu, mutane ba sa   iya zuwa gonakinsu. Saboda haka ba ma son jihar Oyo ta shiga irin wannan hali, da jihar Benuwai ta shiga. Ta yadda za a zo ana haddasa gaba tsakanin makiyaya da manoma.  Wannan abu bai zamo mai dadi ba.  Domin Allah ya hada mu zama da juna.

  Saboda haka yanzu muna nan muna shawarwari kan matakan da za mu dauka. Idan muka ga sun tsaya kan bakansu, kan wannan al’amari, a matsayinmu na masu bin doka da oda da kundin tsarin mulkin Najeriya, za mu iya fuskantar neman hakkinmu a kotu. Idan kotu ta ce kafa wannan doka ya yi daidai, a hana mu walwala a cikin Najeriya. Za mu saurari abin da za a yi. Kamar yadda muka kai karar gwamnatin jihar Taraba. Kuma wannan kara da muka kai gwamnatin jihar Taraba, babu wani daukar fansa ko zubar da jini  ko fada a Taraba. Gwamnatin Taraba tana cewa tana nan tana shirin aiwatar da wannan doka, amma har yanzu saboda wannan kara da muka kai kotu, ba a sami abin da ake so ba. Don haka ba za mu yarda a kafa wannan doka ta hana kiwo a Jihar Oyo ba, amma ba ta hanyar rikici ko rigima ba. Za mu ki yarda da wannan doka ne, ta hanyar doka da oda.

  GTK: Wanne kira ko sako ne kake da shi zuwa ga gwamnatin jihar Oyo da kuma su al’ummar Fulani makiyayan  wannan jiha?

  Bayari: Abin da muke fada shi ne ita gwamnatin jihar Oyo. Idan da gaske take yi kamar yadda suke cewa suna son a yi kiwon zamani ne. Muna son mu shaida masu cewa babu yadda za a yi kiwon zamani ba a yi noman zamani ba. Domin a noman zamani ne kamar a kasashen Turai mutum daya zai noma hatsi buhu miliyan 5. Idan ka dauki karmamin irin wannan manomi zai iya ciyar da shanu miliyan 2, a wata 6 ko shekara 1. Mu kuma yanzu ba mu da irin wadannan manoma a Najeriya. Idan ka daure shanunka mene ne za ka ba su su ci?

  Don haka mu abin da muke cewa shi ne idan ana son a yi kiwon zamani a Najeriya to a fara noman zamani a Najeriya tukuna. Idan aka yi noman zamani muka ga yawan abincin dabbobi da za mu samu daga wajen manoma.

  Kuma ya kamata kafin a ce za a canza mana yadda muke kiwo a Najeriya. A dauke mu a kai mu wajen da ake wannan kiwo na zamani, don a koya mana. Ko kuma a gayyato mana wadanda suke wannan kiwo na zamani, su zo nan Najeriya su koya mana. Ko kuma gwamnatocin da suke son a yi kiwo na zamani, su tura ma’aikatansu kasashen da suke kiwon na zamani, don su koyo su dawo su koya mana.

  Idan ba haka za a yi ba, ya kamata a kyale mu mu ci gaba da rayuwar kiwon gargajiya da muka saba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here