Matsalar Tabin Hankali Yasa Aka Tsare Hassana Na Yan Watanni Ba Shekaru 2 Ba – Kwamared Adamu

0
461

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A SAKAMAKON rade-radin zargi da yamudidi da wasu al’umma a gari ke yi dangane da lamarin wata mata wacce ake dauka da yar yarinya wanda wani yayansu ya tsare ta ko ya kulle ta har na tsawon shekaru biyu a wani daki inda suke a gundumar Rigasa kaduna, wani yayanta Kwamared Adamu Sale ya karyata wannan zargin da cewa kanwar ta su Hassana Sale ba ta wuci watanni uku zuwa hudu a tsare ba.

Kwamared Adamu ya bayyana hakan ne a hirar sa da wakilinmu inda ya bayyana cewa kanwarsu Hassana wacce ke da akalla sama da shekaru talatin da biyar da haihuwa, ta samu matsalar tabin hankali ne bayan aurenta na farko wanda anan ne ta ke da yara har hudu kamin mutuwar auren na ta wanda ya yi sanadin samun matsalar na ta.

Kwamared Adamu Sale Dan uwan Hassana kenan

Ya kara da cewa dubi da irin yanayin da Hassanan ta shiga bayan mutuwar auren na ta na farko akalla shekaru biyu da suka gabata, hakan ya sanya suka shiga neman mata magani tun a wannan lokacin wanda cikin ikon Allah, Allah Yasa ta samu saukin da har ta sake yin wani auren bayan wannan matsalar da ta fuskanta.

Ya ce “toh bayan auren na ta na biyu wanda ba ta wuce wata biyu da yin auren ba, sai muka samu labarin cewa ciwon nan na ta ya sake tashi wanda har ya kai ga ta gudu ta bar gida inda sai da ta samu watanni shida ba a san inda ta ke ba, kamin Alllah Yasa daga baya a ganta inda wasu suka kirani suka bayyana mun lokacin ina kasuwa, don a hannun yan sandan bakin ruwa na amshe ta.”

Acewarsa, Hassana ta kasance ta na zaune ne a gidan wani babban yayansu Malam Lawal wanda kuma shi ne babba a dakinsu da suke uwa daya uba daya, sakamakon wani zama da su ka yi da shi da sauran yan uwan nasu inda suka amince da barin na ta a hannun shi don kulawa da ita yayin da suka cigaba da neman mata magani.

Kwamared Adamu ya ci gaba da cewa, bayan bayyanar na ta da Allah Yasa aka ganta, sun yi yunkurin nema mata magani ta hanyar kai ta wajen wani kwararrren likita dake asibitin Malam Bala a cikin garin Rigasan, wanda ya kuma tabbatar musu da cewa matsalar na ta ba wani abu bane illa ciwon rabuwa da tsohon mijin na ta wanda inda Allah Zaisa ta koma za ta iya samun lafiya.

Ya kara da cewa su karan kansu basu jidadin yanayin yadda aka bar ita kanwar ta su Hassana ba, domin inda sun samu labarin hakan tun farko da zasu dauki mataki akai, to amma saboda dukkansu ba gida daya suke zama da shi wannan yayan nasu ba kuma basu zaci abubuwan zasu kasance hakan ba dubi da shi ma mutum ne mai iyali wanda har yake da yara sama da talatin da mata hudu, yasa basu damu ba.

A nata jawabin, matar yayan nasu Malama Hauwa ta bayyana wa wakilinmu cewa suna iyakar bakin kokarin su wajen kare hakkin ta da ganin sun kula da ita daidai gwargwado dukda irin matsalar da ita Hassanan ke fama da ita da kuma irin kalu balen tirjiya da suke fuskanta a yayin ba ta abinci ko yi mata wanka.

Ta ce “ a duk lokacin da mu ka yi kokarin shiga mu ba ta abinci, ta kan maka mutane da cizo ko ta rika yakushin mutum ballantana ace mun fito da ita za mu yi mata wanka, to kuma kun ga karfin mu da nata ba zaiyo daya, shi yasa muke mika mata abinci wani lokacin ta taga.”

Acewarta, tun farko a duk lokacin da su ka yi yunkurin fito da ita don yi mata wanka ko kai ta yin bayan gida, Hassana kanyi yunkurin rugawa waje da gudu da niyar tsirewa wanda ta taba yin hakan, inda sai dakyar aka samu wasu samari a unguwar suka kamo musu ita, wanda hakan yasa suke jin tsoron barin ta domin ta fito ta zauna cikin su.

Hakazalika acewar dan uwan nata Adamu, su basu ga laifin wanda yaje ya sanar da ita wannan mata Hajiya Rabi halin da ita wannan kanwar tasu ta ke ciki ba domin ko da su ka je suka zanta da ita matar, sun fahinci juna kana basu bukaci ta bayyana musu ko wani makwabcin nasu bane ya sanar da ita dukda sunso ace da su yan uwanta ya fara nema ya sanar dasu ya ga ko ba zasu dauki wani mataki akai ba kamin yaje ko’ina ya sanar da wasu.

A karshe yayan nata Kwamared Adamu Sale, ya yaba da kokarin da ita wannan mata Hajiya Rabi wacce ta kawowa kanwar ta su agaji ta yi kai tsaye bayan ta tabbatar da sahihancin labarin, da kuma ita gwamnatin Jihar Kaduna da ta amshi ragamar cigaba da kula da ita Hassanan, amma ya roki gwamnatin da ta yi afuwa na sako musu wannan dan uwan nasu Malam Lawal ko dan saboda iyalen shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here