Buhari Ya Yi Wa Atiku Ta’aziyyar Rasuwar Shakikin Hadiminsa, Umar Pariya

0
393

Daga Usman Nasidi.

SHUGABA Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a kan rasuwar tsohon hadiminsa na kut-da-kut, Umar Pariya.

Shugaban kasar ya wallafa wannan sakon ta’aziyyar ne ta shafinsa na Twitter @Mbuhari.

A sakon ta’aziyarsa kan rasuwar, Shugaba Buhari ya ce: “Na yi juyayin samun labarin rasuwar shakikin hadiminka, Alhaji Pariya.

“Rasa shakiki da aka kwashe shekaru tare abu ne mai matukar sosa zuciya. Ina addu’ar Allah Ubangiji ya baka hakurin jure rashinsa.

“Allah ya kuma bawa iyalansa hakurin rashinsa, ya yafe masa kurakurensa ya kuma saka masa a kan ayyukansa na alheri a gobe kiyama.”

Mista Pariya ya rasu ne a ranar Talata a wani asibiti dake birnin Dubai bayan fama da rashin lafiya.

Atiku Abubakar ya yi takarar zabe na kujerar shugaban kasa da Buhari inda ya sha kaye kamar yadda sakamakon da Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar suka nuna.

Bayan bayyana sakamakon zaben, tsohon mataimakin shugaban kasar da ya yi takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP ya garzaya kotu domin kallubalantar nasarar Buhari.

Sai dai Atiku Abubakar bai samu nasara ba a kotun zabe da kotun koli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here