EFCC Ta Kama Kansila Da Ya Yi Damfarar Naira Miliyan 2.3 A Kaduna

0
338

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

HUKUMAR yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da wani kansila a gaban kotun jahar Kaduna, a kan tuhumarsa da laifin damfarar kudade da suka kai N2,310,000.

EFCC ta gurfanar da Theophilus Madami ne a gaban babbar kotun jahar Kaduna dake karkashin jagorancin Alkali Darius Khobo bayan kwashe tsawon kwanaki a gidan yarin Kaduna.

Madami, wanda a yanzu hansila ne mai ci dake wakiltar mazabar Kakuri Hausa cikin karamar hukumar Kaduna ta kudu ya damfari wani mutumi, manajan gidan taro, Extra Events Center wanda kansilan ya nemi ya kawo masa kayan kade kade da kudinsa ya kai N2,310,000.

Sai dai koda manajan ya kawo masa kayan bayan ya bashi N200,000, kansilan bai sake bashi ko sisi ba, bayan tsawon lokaci yana tambayarsa kudinsa, sai kansilan ya bashi takardar cirar kudi watau Cheque, da nufin ya tafi banki ya amshi N2,310,000, amma ashe takardar bogi ya bashi.

Da ya sake komawa wajen kansilan, sai ya sake bashi wani sabon takardar cire kudin, amma da ya tafi bankin sai bankin suka tabbatar masa da cewa babu isassun kudi a asusun bankin.

Sai dai koda aka karanto masa laifukansa a gaban kotun, sai Madami ya musanta dukkanin tuhume tuhumensa, daga nan sai lauya mai kara P.C Onyeneho ya nemi kotu ta dage sauraron karar tare da garkame wanda ake kara, amma lauyan wanda ake kara, R.J Dakun ya nemi kotu ta bada belin kansilan.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai Alkalin kotun, Khobo ya bada belin wanda ake kara a kan kudi naira miliyan 2, sa’annan sai ya kawo mutum daya da zai tsaya masa, amma dole sai mutumin yana da gida a Kaduna.

Daga karshe Alkali Khobo ya bada umarnin a mayar da kansila Madami zuwa gidan yari har sai ya cika sharuddan beli kafin a sako shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here