Home Kasuwanci Hukumar NAFDAC ta rufe gidajen Biredi da Na ruwan Leda 47 a...

Hukumar NAFDAC ta rufe gidajen Biredi da Na ruwan Leda 47 a Maiduguri

0
325
Hukumar kula da safarar abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), ta bayyana  daukar matakin rufe gidajen gasa burodi 22 hadi da masana’antun sarrafa ruwan leda (pure water) guda 25, a wani rangadin da ta gudanar a birnin
Maidugurin jihar Borno.Bayanin daukar matakin ya fito ne daga bakin Kodinetan hukumar a jihar Borno, Nasiru Mato, a sa’ilin da yake tattauna wa da manema labarai, jim
kadan da kammala rangadin, ranar Lahadi a Maiduguri.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa sun kulle wasu daga cikin gudajen ne bisa yadda suka kasa cika ka’idojin hukumar kafin fara gudanar da ayyukan su, inda wasu kuma suka gaza wajen zuwa su yi rijista da hukumar baki daya.

Ya ce, “Kafin hakan mun yi amfani da hanyoyin tattara bayanai tare da gudanar da bincike da aiwatar da ganawar keke da keke da jama’ar da ke
amfani da kayayyakin inda suka nuna korafi tare da ankarar da masu gidajen. Wanda babbar manufar daukar matakin shi ne don mu tabbatar mun kare lafiyar jama’a”.

“Sannan ko a cikin yan kwanakin nan sai da muka gudanar da kai ziyarori don  wayar da kan jama’a, a wuraren ibada a duk fadin jihar Borno. Yayin da kuma muka ziyarci masallatai da coci-coci kimanin 20 don mu wayar da kan jama’a dangane da hatsarin shan miyagun kwayoyi da alamun da ake gane magungunan jabu”.

“Haka nan  kuma mun kai wannan ziyara a gidajen burodi da na sarrafa ruwan leda ba tare da mun sanar da masu gudanar dasu ba, wanda mun yi haka ne don samun kyakkyawan sakamako a binciken namu, wajen gano yanayin tsabta tare
da bin ka’idojin NAFDAC sau da kafa”.

Har wala yau kuma, ya ce, “a ziyarar da muka kai a gidajen burodin, ya jawo mun dauki matakin kulle guda 22, bisa dalilin karya dokokin mu daban-daban. Wanda da yawa laifukan su na rashin rijista ne da rashin sabunta rijistar, inda muka samu wasun su da laifin rashin tsabta”.

“Haka zalika kuma, laifukan da muka tarar a wadansu gidajen burodin shi ne
yadda suke amfani da wasu kayan hadi masu hatsarin gaske ga lafiyar jama’a;
wanda ke jawo kamuwa da cutar daji”.

“A hannu guda kuma, a bangaren gudajen sarrafa ruwan leda, mun kulle gidajen har guda 25, saboda yadda suka gaza wajen cika ka’idojin gudanar da
su, musamman ta inda masu gidajen suka kasa kyautata wadannan kayan da suke sayar wa jama’a”.

“Saboda duk kayan da ka ga ba su dauke da tambarin rijistar hukumar NAFDAC,
to kawai ka jefa su a cikin jerin kaya yan jabu”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: