Home Kasuwanci Hukumomin NAFDAC da NDLEA kowaccensu ta samu tallafin motar aiki daga gwamnatin...

Hukumomin NAFDAC da NDLEA kowaccensu ta samu tallafin motar aiki daga gwamnatin Yobe

0
386
Don samun saukin gudanar da ayyukan su cikin tsanaki, a kokarin su wajen dakile bazuwar miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da magance matsalar shigo da gurbatattun kayan abinci da magungunan a Nijeriya, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya bai wa hukumar NDLEA hadi da takwar ta; NAFDAC kyautar motocin aiki kirar Hilux.
Mika wadannan motocin aikin, an yi shi ne biyo bayan bukatar da hukumomin suka nuna, domin samun damar aiwatar da ayyukan su a jihar.
Da yake mika kyautar motocin, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Baba Mallam Wali, a madadin Gwamnan jihar, ya ashaidar da cewa gwamnatin Buni ta zaku matuka dangane da sha’anin tsaro da kare rayuwar yan jihar Yobe tare da dukiyoyin su; a bare guda kuma da aikin ba dare ba rana wajen kyautata jin dadi da walwalar al’ummar jihar Yobe.
Bugu da kari kuma, Gwamna Mai Mala Buni ya kara da cewa, ya yi imani kan cewa babban jigon ci gaban samun walwalar jama’a da yaduwar arziki yana ta’alaka ne da wadatacciyar lafiyar al’ummar jihar Yobe. Ya nanata cewa, bisa ga wannan ya zama wajibi gwamnatin jihar ta yi iya kokarin ta wajen duba bukatun hukumomin tsaron, da duk abinda zai taimaka domin su gudanar da ayyukan su cikin tsanaki.
“A matsayin mu na wadanda makamancin wannan nauyin ya hau kan mu, ba zamu taba gajiya wa ba, wajen bayar da gudumawar da ta dace ga bangarorin jami’an tsaro ba, matakin da zai taimaka, wajen samun tabbacin dawamamen zaman lafiya ga al’ummar mu, a kowane lokaci buqatar hakan ta taso”. In ji shi.
A hannu guda kuma, Gwamnan ya mika wasu qarin kyautar motocin aikin tsaro guda tara ga yan banga, domin samun saukin gudanar da aikin taimakon jami’an tsaron aikin yaki da matsalar tsaron Boko Haram a jihar.
A nasu vangaren, wakilan kwamandojin hukumomin NDLEA, NAFDAC hadi da na qungiyar yan banga, dake jihar Yobe, sun yaba da kokarin gwamnatin jihar, bisa goyon bayan da suke samu daga bangaren ta, inda kuma suka sha alwashin amfani da motocin ta hanyar da ta dace.
Haka zalika kuma, gwamnatin jihar ta mika kwatankwacin wadannan motocin ga Bataliya ta 27 Task Force Brigade, ta rundunar sojojin Nijeriya haxi da sabuwar rundunar yan-sandan ‘Haba Maza’, domin samun damar gudanar da aikin tsaro a fadin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: