Gwamnatin Kano Na Nazarin Hukuncin Kotu

0
380
Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNATIN jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa ya zuwa yanzu tana nan ta fara yin nazarin hukuncin da wata babbar kotu ta yanke a kan batun masarautu hudu da gwamnatin jihar ta kirkiro a kwanan baya.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Kwamared Muhammad Garba ne ya bayyana hakan, inda ya ce hakika sun samu cikakken labari a game da wannan hukuncin amma ya zuwa yanzu suna kokarin yin nazarin hukuncin kasancewar majalisar dokokin jihar ce ta aiwatar da dukkan tsare-tsaren doka har aka samar da su.
Gwamnatin ta kuma umarci jama’a da su kwantar da hankalinsu domin gwamnatin na nan tana son yin abin da ya dace bayan kammala nazarin hukuncin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here