Zan Dauki Mataki A Kan Yari___  Bello Muradun

0
437
Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNATIN jihar Zamfara da ke ikirarin samun nasara kan matsalar tsaron jihar ta dora laifin sabbin hare-haren da aka kai na baya-bayan nan kan tsohon Gwamnan jihar.
Gwamna Bello Muhammad Matawalle wanda ya ce ya yi sulhu da wadanda gwamnatinsa ta ke ganin sun addabi jihar, ya zargi wanda ya gada Abdulaziz Yari da yin zagon kasa ga sha’anin tsaron jihar.
Ya ce tsohon Gwamnan yana bakin ciki da zaman lafiyar da aka samu wanda ya kasa magancewa shekaru 8 na mulkinsa.
Kana Gwamnan ya yi zargin cewa duk lokacin da Abdulaziz Yari ya ziyarci jihar sai an kai hari kuma ya yi barazanar cewa zai dauki mataki a kan tsohon Gwamnan idan aka sake kai hari lokacin da ya shiga jihar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here