Ba na Sha’awar Zarcewa A Mulki Karo Na 3 – Shugaba Buhari

0
405

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da sha’awar zarcewa a kan karagar mulkin Najeriya a matsayin shugaban kasa da sunan neman wa’adin mulki na uku.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wanda ke gudana a yanzu haka a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa dake babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Blue Print ta ruwaito.

Wannan batu na shugaban kasa ya karyata rade radin da wasu yan siyasa ke yin a cewa shugaba Buhari na neman zarcewa da wa’adin mulki na uku kamar yadda tsohon shugaban kasa
Olusegun Obasanjo ya yi, inda wasu ke zargin Buhari na wannan shiri ne da hadin bakin yan majalisu.

A jawabinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar ma mahalarta taron cewa zai tattara inasa inasa ya bar fadar gwamnatin Najeriya zuwa shekarar 2023 a karshen wa’adin mulkinsa na biyu saboda kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta neman wa’adin mulki na uku.

Buhari ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar APC dasu mayar da hankali a mazabunsu, tare da tabbatar da sun mamaye mazabunsu a siyasance ta yadda zasu zama masu fada a ji, domin kuwa abin kunya ne a ce APC ta rushe bayan karewar wa’adin mulkinsa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon shugaban wucin gadi na jam’iyyar APC, Bisi Akande, gwamnoni da sauran manya manyan jiga jigan jam’iyyar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here