Babban Burina Na Inganta Walwalar Duk Wani Dan Najeriya – Inji Buhari

0
296

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya himmatu matuka wajen habbaka walwalar yan Najeriya tare da inganta rayuwarsu, kamar yadda ya bayyana wa taron gwamnonin jam’iyyar APC a garin Jos na jahar Filato.

Shugaban kasa ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin taron tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC inda aka tattauna a kan tsare-tsaren gwamnati.

Buhari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa gwamnatinsa na alfahari da nasarorin da ta samu na tayar da komadar tattalin arzikin kasa bayan shiga halin tabarbarewa a baya.
Shugaban kasa ya ce a yanzu haka Najeriya ta hau hanyar samun ci gaba mai daurewa tun shekaru hudu da suka gabata, musamman ta bangaren ci gaban al’umma, samar da manyan ayyuka da kuma alkhairai daban-daban.

“Sakamakon fahimtar muhimmancin mawuyacin hali da jama’a ke shiga, musamman wadanda ibtila’I ko rikici ya rutsa da su, na samar da sabuwar ma’aikata wanda na mika wa jami’in gwamnati mai mukamin minista domin ya jagoranta.

“Wannan ya nuna manufar gwamnatina na rage radadin matsalolin da ‘yan Najeriya suke fuskanta, musamman marasa karfi. Alkalumma sun tabbatar da tun daga shekarar 2015, gwamnatinmu ta samu ci gaba a fannoni daban-daban, kuma a shirye muke mu ninka kokarinmu.” Inji shi.

Shugaban kasa ya jaddada wa gwamnonin APC manufarsa na kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar nan. Sa’annan ya danganta dukkanin nasarorin da ya samu ga goyon bayan da gwamnoni suke ba shi.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku  Bagudu ya bayyana cewa suna hada kai da gwamnatin tarayya ne domin su inganta rayuwar dan Najeriya. Taron ya samu halartar gwamnonin APC 8 da mataimakan gwamnoi guda 3, sai kuma ministoci 2, da shugaban jam’iyyar APC na kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here