Gwamna Matawalle Ya Rike Min Kudin Fansho Da Alawus – AbdulAziz Yari

0
452

Daga Usman Nasidi.

TSOHON Gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya bayyana cewa magajinsa, Gwamna Bello Matawalle, ya hana shi kudin fansho da alawus dinsa a matsayin tsohon Gwamna kamar yadda dokar jihar ta tanada.

A wasikar da ya aika wa gwamnan, Abdulaziz Yari, ya bukaci Gwamna Matawalle ya biya shi kudaden saboda babu wani dalilin da zai sa ya rike masa kudi.

Yari ya ce tun da ya sauka daga mulki, sau biyu kacal aka biya shi kudin kula da kansa na N10m a wata.

Ya ce dokar jihar ta tanadi bai wa tsaffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, tsaffin kakakin majalisa, da mataimakansu, alawus a kowane wata.

A cewarsa : “Ina son jawo hankalinka kan wannan dokar da aka gyara kuma aka rattaba hannu ranar 23 ga Maris, 2019.”

“Dokar ta tanadi cewa daga cikin abubuwan da tsohon Gwamna ya cancanta shi ne alawus na wata milyan goma (N10,000,000) da fansho daidai kudin albashin da yake dauka lokacin da yake mulki.”

“Saboda haka, ina mai sanar da kai cewa tun lokacin da wa’adina ya kare a ranar 29 ga Mayu, 2019, sau biyu kadai aka biya ni kudin; watan Yuni da Yuli kuma ba a biyani kudin fanshon watan Yuni ba.”

A bangare guda, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta musanta zargin da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, AbdulAziz Yari, cewa yana goyon bayan ‘yan bindigan da suka addabi jihar tun lokacin da yake gwamna.

A makon jiya, wasu ‘yan bindiga sun hallaka akalla mutane 18 a garin Karaye da ke karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya tuhumi magabacinsa, AbdulAziz Yari, da laifin yi wa yunkurin kawo zaman lafiya zagon kasa cikas duk lokacin da ya ziyarci jihar.

Gwamnan ya yi barazanar daure Yari idan ya sake shiga jihar Zamfara ya tayar da tarzoma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here