Jabiru A Hassan, Daga Kano.
GIDANIYAR Yakubu Dan mono dake Tofa ta fara bada tallafi ga dalubai ‘yan asalin yankin masu karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu domin ganin ana taimakawa fannin ilimi a karamar hukumar.
Wakilinmu, ya ruwaito cewa tuni aka fara aikin tantance daliban da suka cike takardar neman tallafin gidauniyar, wanda ya zuwa yanzu an sami nasarar tantance dalubai 94 sannan an ba da tallafin kudi ga dalubai 36 kana an amince a bada tallafin kudi ga dalibai 64 domin suma su amfana da shirin gidauniyar na tallafa wa karatu cikin yardar Allah.
Daliban da suka zanta da Albishir watau Hassan Sani Umar da Hassana Habibu da kuma Lawan Uba Umar sun bayyana cewa wannan gidauniya tazo daidai lokacin da ake bukatar ta, sannan sun jinjinawa shugaban gidauniyar watau Dokta Nafi’u Yakubu Tofa bisa wannan tunani da yayi na kafa ta domin tallafawa dalubai maza da mata batare da nuna gjiyawa ba.
Shima a nasa bayanin shugaban kwamitin tantance dalubai na gidauniyar Dokta Junaidu Yakubu Mohammed ya ce za su ci gaba da tantance dalubai ‘yan asalin karamar hukumar Tofa domin ganin sun sami taimako daga gidauniyar ta Yakubu Dan mono ta yadda kwalliya zata ci gaba da biyan kudin sabulu ta fuskar ilimi.
Shugaban gidauniyar, Dokta Nafi’u Yakubu Tofa ya bayyana cewa gidauniyar zata ci gaba da bada tallafin karatu g dalubai ‘yan asalin karamar hukumar Tofa kuma suna duba yiwuwar fadada bad tallafin ga makwabtan yankin kamar kananan hukumomin Rimin Gado da Bagwai da Dawakin Tofa da kuma taimakon marayu kamar yadda yake cikin kudure-kuduren gidauniyar