Hanyar Abuja Zuwa Kano Ta Zama Tarkon Mutuwa

0
542

Rabo Haladu Daga Kaduna

MATAFIYA a Najeriya na kokawa kan rashin kyawun babbar hanyar Abuja zuwa Kano, wadda tana daga cikin manyan titunan kasa da ke sada mutane da jihohi daban-daban.

Ana kokawa kan lalacewar titin ne, wanda da an riga an fita babban birnin tarayyar, to rashin dadin tafiya kuma sai yadda Allah ya yi.

Hanyar dai na cikin manyan hanyoyin da suka shafi rayuwar al’ummar da ke shiyyar arewa maso yammacin ta fuskar kasuwanci da zirga-zirgar jama’a.

Sai dai aikin da ake yi na sake gina hanyar, wanda ake kukan cewa yana tafiyar-hawainiya shi ke haddasa matsaloli, ciki har da aukuwar hadurra da sanadin asarar rayukan jama’a da dukiya.

Alhaji Abubakar Ustaz na cikin shugabannin kungiyar direbobi reshen Jabi a Abuja, ya ce ja baya da aikin ya yi yana janyo matsaloli sosai.

”Lokacin da muka ji shugaban kasa ya bayar da umarnin sake gina hanyar nan muna ta farin ciki da nurna saboda ganin za a raba mu da hadurra, amma sai ga shi kamfanin da aka bai wa aikin ba ya kokarin kammalawa a kan lokaci.

Wani direba ya ce hadarin da ke cikin tafiyar sakamakon rashin kyawun hanyar ya wuce tunani, ”Hanyar nan ta zamo mana tarkon mutuwa, duk inda aka sanya alamar sauya hanya, sai kana tafiya za ka hango babbar mota ta yo kanku.

“Wasu wajen kaucewa suke fadawa cikin hadari, baki daya mu direbobi da fasinja a wahale muke tafiyar, a baya da mu je ajiye fasinja Allah-Allah muke mu juyo, amma yanzu ina, hakan ba mai yiwuwa ba ne.”

”Wahalar da muke sha ta isa, mun yi tunanin da an fara aikin za mu samu sauki amma abin ya wuce tunaninmu, ko ina an tona rami, wajen kauce wa ramukan muke fasa tayoyinmu, a baya daga Abuja zuwa Kano awa hudu ne zuwa biyar amma yanzu awa 10 zuwa 11 muke yi,” in ji wani direban.

Wannan matsalar ta ja hankalin majalisar wakilai  har ta fara daukar mataki don ganin an shawo kan matsalar.

Sun kuma gayyaci kamfanin da aka bai wa kwangilar sake gina hanyar don sanin dalilin da ya sanya aikin ke tafiyar hawainiyar.

Honarabul Abubakar Kabir Abubakar Bichi shi ne shugaban kwamitin ayyuka na majalisar wakilan ya shaida wa manema labarai cewa: ”Gaskiya ne aikin na tafiyar hawainiya, shi ya sa majalisar wakilai ta ce ba za ta zuba ido ana asarar rayuka da dukiya ba.

“Don haka mun kira kamfanin da aka bai wa aikin don mu tattauna mu san yaya aikin ke tafiya, kuma In Sha Allah za mu yi zaman ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamba.”

Tun lokacin kaddamar da aikin hanyar a watan Yunin bara, ministan ayyukan  Babatunde Fashola ya ce sai da gwamnatin tarayya ta yi tanadin kudin kwangilar aikin lakadan, don haka za a yi aiki ne gadan-gadan.

Ya ce za a yi aikin ba tsagaitawa har sai ranar da za a sake haduwa a bikin budewa, amma ga alama wankin hula zai kai dare.

Za a iya cewa matafiya a hanyar Abuja zuwa Kano suna tsaka mai wuya, kasancewar a baya sun guji hanyar don tsira da ransu saboda tabarbarewa tsaro, yanzu kuma rashin kammala aikin hanyar ne ke jefa rayuwar al’umma a cikin hadari.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here