Kamfanin Jirgin Sama Na Birtaniya Ya Gamu Da Matsala A Hanyarsa Ta Zuwa Abuja

0
610

Rabo Haladu Daga Kaduna

KAMFANIN jiragen sama na Birtaniya ya ce wani jirginsa ya samu ‘yar karamar matsalar na’ura yayin da yake sararin samaniya a kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga birnin Landan.

Hakan ya sa matukin jirgin ya juya akalarsa ya koma Landan, inda fasinjoji da ma’aikatan jirgin suka samu tarba daga jami’an bayar da kulawar gaggawa, wadanda suke cikin shirin ko-ta-kwana.

Kamfanin dai ya kai fasinjojin otal, inda suka kwana a can.

Sai dai har yanzu ba a san wace irin matsala jirgin ya samu ba.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here