Daga Usman Nasidi.
KWANAKI kadan bayan Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya soke dokar jihar na biyan tsaffin shugabanin jihar fansho na makuden miliyoyi, jam’iyyar APC a jihar ta bayyana matsayan ta a kan lamarin.
A cewar jam’iyyar ta APC a jihar Zamfara ta ce ta yi maraba da matakin da Gwamnan ya dauka ta kuma yi masa jinjina.
Majiyarmu ta gano cewa mataimakin shugaban jam’iyyar APC a mazabar Central, Alhaji Sani Gwamna ya ce a yi amfani da kudaden da za a samu bayan soke dokar wurin yi wa al’ummar Zamfara ayyukan ci gaba.
Gwamna ya bayyana hakan ne a ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba bayan taron da jam’iyyar ta gudanar.
Jam’iyyar ta APC ta ajiye adawa a gefe guda ta yaba wa matakin da Gwamnan jihar ya dauka duk da cewa yana jam’iyyar PDP ne.
A baya, Gwamna Matawlle a ranar Laraba 27 ga watan Nuwamba ya saka hannu kan sabuwar doka da ta shafe tsohuwar dokar na ba wa tsaffin shugabanin miliyoyin kudi a matsayin fansho.
A jawabinsa yayin saka hannu kan dokar, Gwamna Matawalle ya ce za a yi amfani da kudaden wurin yiwa al’ummar jihar ayyukan cigaba da samar da ayyukan yi ga matasa a jihar.