Buhari Ya Bayar Da Umurnin A Sake Gaggauta Daukan ‘Yan Sanda 400,000

0
295

Daga Usman Nasidi.

MA’AIKATAR kula da harkokin da suka shafi rundunar ‘yan sanda ta ce ta samu umurnin gaggawa daga fadar shugaban kasa a kan ta dauki sabbin ‘yan sanda 400,000 domin magance karancin da jami’an tsaro keda shi.

Da yake sanar da hakan ranar Litinin, shugaban sashen hulda da jama’a na ma’aikatar, Odutayo Oluseyi, ya bayyana cewa tuni ministan ma’aikatar kula da harkokin ‘yan sanda ya kafa kwamitin mutane 13 domin fitar da tsarin yadda za a dauki karin sabbin jami’an.

Umurnin fadar shugaban kasar ya kawo karshen tababar da ake yi a tsakanin hukumar kula da harkokin ‘yan sanda (PSC) da kuma ofishin babban sifeton rundunar ‘yan sanda (IGP) a kan waye yake da alhakin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda.

Oluseye ya bayyana cewa kwamitin da ministan ya kafa ya kunshi mambobi daga PSC da kuma rundunar ‘yan sanda.

Ya kara da cewa aikin kwamitin shi ne fito da tsarin da za a yi amfani da shi wajen daukar sabbin jami’an bisa tsarin gwamnatin shugaba Buhari na ba wa tsaro fifiko.

A cewar Oluseye tuni minista Dingyadi ya rantsar da kwamitin tare da sanar da cewa daukan sabbin jami’an na daga cikin shawarwarin da kwamitin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayar a kan aiyukan da ya kamata gwamnati ta ba wa fifiko domin cimma manufofinta kamar yadda ta dauki alkawari tun lokacin yakin neman zabe.

Shugaba Buhari ne ya kafa kwamiti a karkashin Osinbajo domin duba nasarorin da gwamnatinsu ta samu da kuma haska mata bangarorin da ya kamata ta mayar da hankali a zangonta na karshe, daga 2019 zuwa 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here