El-Rufai Ya Yi Martani Ga EFCC Kan Zargin Batan N32bn A Yayin Da Yake Ministan FCT

0
355

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A ranar Lahadi, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna yace bai taba hana hukumar yaki da rashawa ta EFCC da ta yi aikinta ba. A maimakon hakan, ya garzaya kotu ne don wanke kanshi.

A takardar da lauyan El-Rufai, A.U Mustapha (SAN) ya fitar, ya ce gwamnan jihar Kaduna ya tunkari kotun ne a 2009 don ya wanke sunansa daga baci.

Mustapha ya ce, “EFCC ta baza a kafafen yada labarai yadda N32bn ta bace, lamarin da yasa Malam El-Rufai ya nufi kotu don bayani dalla-dalla.”

Idan za mu tuna, takardar ta bayyana yadda El-Rufai lokacin da yake ministan tarayya ya siyar da wasu filaye a Abuja. Ya kuma shugabanci siyar da wasu gidajen a babban birnin tarayyar, wanda hakan ya kawo wa gwamnatin tarayyar kudi har naira biliyan 32.

Lauyan El-Rufai ya tunatar da cewa, tsananin siyasantarwa ce ta sa hukumar yaki da rashawa ta EFCC din ta ke shafawa mutane kashin kaji.

Babban lauyan ya ce, El-Rufai ya garzaya kotu ne don tantance abubuwa uku masu muhimmanci. kamar haka, “Kotun ta tantance mai kara, wanda a lokacin da yake ministan tarayya ko ya bi sharuddan da majalisar zartarwa ta tarayya ta gindaya na siyar da gidaje daga watan Mayu 2005 da watan Mayu 2007.”

Mustapha ya kara da cewa, El-Rufai ya bukaci abubuwa guda 7 daga kotun wadanda suka hada da “takardar shaidar cewa an siyar da gidajen gwamnatin tarayyar kamar yadda majalisar zartarwa ta tarayya ta gindaya ta hannun kwamitin wucin-gadin da ta nada na siyar da gidajen”.

Lauyan El-Rufai ya ce, “Muhimmin abu a nan shine, kotun ta ba da duk bayanan da wanda muke karewa ya bukata kuma mun gamsu da hakan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here