Gwamna Matawalle Ya Fitar Da Dalibai 200 Kasar Waje Don Karo Ilimi

0
401

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya sanar da gwamnatinsa ta dauki nauyin matasa 200 ‘yan asalin jahar Zamfara domin yin karatu a wasu jami’o’ da ke kasashen duniya guda.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga daliban da suka samu nasarar samun wadannan duraben karatu a karkashin tsarin ba da tallafin ilimi na gwamnatin jahar Zamfara, inda ya yi kira a gare su da su kasance ”yan kasa nagari masu kishin jaharsu a inda za su tafi karatun.

A jawabinsa, Gwamnan ya ce daga cikin daliban akwai guda 30 da za su yi karatu a kasar Indiya, guda 50 a kasar Sudan, guda 50 a kasar Chaina da kuma guda 70 a kasar Cyprus, kuma dukkaninsu za su karanci fannonin da suka danganci kiwon lafiya da kuma kimiyya da fasaha ne.

“Burina ne na inganta fannin ilimi a jahar Zamfara, musamman abin da ya shafi harkar matasa, shi ya sa ma daga cikin nade-naden da na fara yi a gwamnatina akwai ofishin mai bai wa Gwamna shawara a kan harkar tallafin karatu da sha’anin dalibai.

“Mun baku wannan dama ne domin fahimtar kwazonku da kuma fatan za ku yi amfani da ilimi da kwarewar da za ku samu wajen sauya rayuwar al’ummar jahar Zamfara tare da kawo ci gaba a yankunanku da ma jahar gaba daya.

“Don haka za ku shiga cikin mummunan tarihi idan har kuka sake kuka yi wasa da wannan dama, kuka kasance tamkar masu yawon bude idanu a kasashen da za ku tafi karatu a maimakon ku yi karatun, don haka nake kira a gare ku ku jajirce wajen yin karatu tare da daukansa da muhimmanci. Mu kuma zamu cigaba da baku duk gudunmuwar da ya kamata don ganin kun samu nasara.” Inji shi.

Daga karshe Gwamnan ya lallashi sauran daliban da suka nemi wannan dama amma ba su samu ba da cewa wannan somin-tabi ne, domin kuwa gwamnatinsa za ta ci gaba da neman ire iren guraben karatun nan domin taimaka ma daliban jahar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here