Fiye Da Naira Biliyan 134 Aka Yi Wa Jihar Borno Kasafin Kudinta Na 2020

0
544
Muhammad Sani Gaza’s Chinade, Daga Maiduguri
GWAMNAN jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya gabatar da kudurin kasafin kudinsa na shekarar 2020 a gaban majalisar dokokin jihar, da ke birnin Maiduguri, a makon nan da muke ciki.
Wannan kudurin kasafin kudin, mai taken ‘sake farfado da al’amurra da karfafawa’, na kimanin Naira biliyan 134,500,923,000, wanda ya zarta na shekarar 2019 da kaso 7.5% a cikin dari. Ya kunshi naira biliyan 67,540, 524,000, daidai da kaso 50.37 don ayyukan gwamnati na yau da kullum, yayin da aka ware naira biliyan  66,960,399,000, kaso 49.7 a manyan ayyuka.
Kasafin kudin ya nuna bangaren kiwon lafiya shi ne ya samu kaso mafi tsoka a kasafin; na kimanin naira biliyan 11,666,873,000, inda ma’aikatar sake farfado da yankunan da matsalar tsaro ta tagayyara ya zo na biyu a kasafin kudi naira biliyan 9,230,418,000.
A lokacin da yake mika daftarin bayanan kudurin kasafin kudin ga zauren majalisar, Gwamnan ya bayyana cewa an samu kari a kasafin kudin wannan shekara ne biyo bayan dadin farashin da danyen man fetur ya samu a kasuwa, daga dalar Amurka 57 zuwa dala 60 a kowace ganga.
Babagana Zulum ya sake bayyana cewa gwamnati tana da muradun shawo kan matsalolin yan gudun hijira a jihar, baya ga kuma kokarin aiwatar da manufofin gwamnatin sa guda 10 wadanda ta sa a gaba, domin fitar da jihar daga halin tagayyara da matsalar tsaro ta jefa jama’a a ciki.
“Sannan kuma, babbar hikimar da ke kunshe da bayyana manufofi da alkiblar gwamnatin mu shi ne domin samun karsashi da qaimi wajen gudanar da ayyukan mu a cikin gaskiya da rikon amana, sadaukarwa domin mu kasance na musamman tare da sanya gamsuwa da nutsuwa a zukatan jama’ar da muke jagoranta, wajen samun zarafin sake gina yankunan mu. Mu samu ikon sake bunkasa yanayin tattalin arzikin jama’ar wannan jihar, mu kirkiro gurabun ayyukan yi da sake inganta tsarin ilimin mu zuwa ga matakin da kowa zai yi alfahari dashi, habaka fannin kiwon lafiya ga al’ummar mu da ke yankunan karkara kuma da aiki don wanzar da zaman lafiya da walwalar jama’a”. In ji Gwamna Zulum.
A nasa bangare kuma, Kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Hon Abdulkareem Lawan bai wa Gwamnan jihar tabbas ya yi, kan cewa yan majalisar za su ba maras da kunya wajen daukar matakin yin aiki tukuru, wajen duba kudurin kasafin, “domin bai wa bangaren zartaswa cikkakiyar dama wajen aiwatar da muhimman ayyukan da kasafin ya kunsa, wanda ‘yan asalin jihar Borno za su ci gajiyar shi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here