Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Lalong

0
267

Isah Ahmed Daga  Jos

KOTUN daukaka kara da ke zama a garin Jos, babban birnin Jihar Filato, ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Simon Lalong. Kotun daukaka karar ta tabbatar da zaben ne, bayan da ta tabbatar da hukumcin da Kotun sauraron kararrakin zabe da ta yi zama a garin Jos ta yi. Na watsi da karar da dan takarar kujerar gwamnan jihar, karkashin jam’iyyar PDP Jeremiah Useni ya shigar a gabanta, sakamakon rashin kawo gamsassun shaidu.

Kotun ta ce Gwamna Lalong ya cancanci ya tsaya takarar kujerar gwamnan jihar a zaben da ya gabata, domin ya gabatar wa hukumar zabe takardar shaidar rubuta jarabawar gama makarantar sakandire, da ya samu a shekarar 1980.

Kotun ta yi bayanin cewa lauyan mai karar, bai iya kawo wa kotun cikakken shaidar cewa Gwamna Lalong bai yi wa hukumar zabe ta INEC, cikakken bayanin kansa ba, a wajen cike takardar tsayawa takarar.

Har ila yau kotun ta ce mai karar bai gamsar da kotun da cikakkiyar shaidar cewa an yi magudi a lokacin wannan zabe ba. Don haka kotun ta yi watsi da wannan kara, tare da tabbatar da hukumcin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi, na watsi da wannan kara.

Jagoran lauyoyin jam’iyyar PDP Barista Edward Pwajok ya bayyana cewa wanda suke karewa da jam’iyyar PDP, ba su gamsu da wannan hukunci da wannan kotu ta yi ba, na watsi da wannan kara. Don haka ya ce za su tafi kotun koli, domin ganin an yi masu adalci.

A nasa bangaren jagoran lauyoyin  APC da Gwamna Lalong, Garba Pwul SAN ya bayyana cewa, a shirye suke su tafi kotun kolin. Domin sun yi imanin cewa hukuncin da kotun kolin za ta yanke, ba zai taba saba abin da kotun sauraron kararrakin zabe, da  kotun daukaka karar da hukumar zabe suka yi ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here