Masaratu: Majalisar Dokokin Kano A Yau Ta Kasa Cimma Matsaya

0
369

Daga Z A Sada 

ZAMAN da majalisar dokokin jihar Kano ta yi a yau kan duba dokar kirkiro sababbin masarautu ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.

Yayin zaman, ‘yan majalisar sun yi muhawara kan dokar har na tsawon sa’a uku a kebe ba tare da ‘yan jarida ba.

Sai dai ba su samu yadda suke so ba, yayin da suka yi yunkurin yi wa dokar karatu na biyu a yau din biyo bayan kammala karatu na farko.

Sai dai sun ci alwashin ci gaba da duba dokar a zamansu na gobe Alhamis.

A gefe guda kuma, wasu daga cikin ‘yan majalisar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar sun yi yunkurin sukar dokar a zauren majalisar amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, inda suka rika daga hannu amma aka hana su damar yin magana ba.

PDP tana da ‘yan majalisa 12 ne kacal cikin 40 a majalisar, abin da ke nufin ba za su iya kawo tsaiko ga dokar ba saboda ba su kai biyu bisa uku ba, wanda shi ne yawan ‘yan majalisar da doka ta tanada su amince kafin yin wata doka.

Idan za a iya tunawa dai a ranar 21 ga Satumban 2019 ne Mai Shari’a Usman Na’abba na babbar kotun jihar Kano ya soke dokar farko da majalisar ta yi na kirkiro masarautun Karaye da Gaya da Bichi da Rano, inda ya ce ba a bi ka’ida ba yayin yin ta.

Daga nan ne kuma ‘yan majalisar suka daura aniyar sake yin dokar ta hanyar da ta dace bisa kudirin da gwamnati ta aike masu. A baya dai cikin kwana daya aka kai kudiri kuma aka kaddamar da dokar.

Masarautar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here