Matukan Keke Napep Sun Gudanar Da Zanga-zanga A Maiduguri

0
364
Rabo Haladu Daga Kaduna
 MATUKAN a daidaita sahu ko KEKE NAPEP sun gudanar da zanga-zanga a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, don nuna rashin amincewarsu da shirin dakatar da ayyukansu da gwamnatin jihar ke shirin yi.
A yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 a zauren majalisar dokokin jihar Borno, Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanar da cewa, nan da 20 ga watan Janairu 2020, gwamnati za ta takaita ayyukan masu KEKE NAPEP din a manyan hanyoyin jihar.
Gwamnan jihar Babagana Zulum ya kira taron gaggawa da shugabannin kungiyoyin matukan keken mai kafa uku don fayyace bayanai game da ayyukan nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here