Mun Shirya Tsaf Domin Fara Jigilar Masu Zuwa Umrah- Mustapha Hamisu

0
372
Rabo Haladu Daga Kaduna
KAMFANIN jigilar Hajji Da Umrah da sauran kasashe, da ke jihar Kano, mai suna HAMSYL TRAVEL AGENCY AND TOURS ya bayyana cewa sun kammala shiri don jigilar masu zuwa aikin Umrah a kasa mai tsarki.
Kamfanin ya ce sun tanadi masaukai a Madina da Makkah da kuma jirage domin kyautata wa wadanda za su aikin Umrah, wanda hakan yana daga cikin matakan da suka dauka don saukaka wa wadanda suka tafi aikin Umrah.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Babban Manaja na kamfanin Alhaji Mustapha Hamisu, a wata zantawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke Kano, inda ya ce yanzu haka sun fara bada Viza ga wadanda za su tafi aikin Umrah, yana mai cewa kamfaninsu ya kammala duk wani shiri ga masu zuwa aikin Umrah.
Da yake bayani a kan matsalar mata ‘yan share wuri zauna wadanda suka fakewa da zuwa Umrah ko aikin Hajji daga bisani su ki dawowa gida Nijeriya, ya ce suna daukar matakan da suka kamata domin magance matsalar a kamfaninsu wanda a cewarsa, suna sane da matsalar.
A kan hakan , Alhaji Mustapha Hamisu, ya ba wa abokan huldarsu tabbatacin cewa duk wanda ya yi hulda da HAMSYL Travel Agency zai gamsu kwarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here