MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
WANI babban fadan cocin Darikar Katolika da ke Anaca jihar Anambra mai suna Rabaran Uche Ukor ya yanke jiki ya fadi ranar Laraba a garin Asaba jihar Delta lokacin da yake tare da ‘yan uwansa yana bayar da horo ga kungiyar da za ta wakilci cocinsa a wani wasan kwallon kafa na sada zumunta da aka shirya tsakanin cocinsa da na abokan aikinsa.
Wata majiya da ke cocin ta tabbatar wa wakilinmu na kudanci faruwar hakan inda ta ce “Tabbas Rabaran Ukor ya yanke jiki a filin wasan lokacin yana horas da ‘yan wasa yana tsakiyar ba ‘yan wasan horo aka ga kawai ya fadi yana yin numfashi sama-sama daga bisani ya ce ga garinku nan”.
Majiyar ta ci gaba da cewa “wasan kwallon kafa na sada zumunta ne aka shirya tsakanin cocin Anaca da na shiyyar Issele Uku, jihar Delta
.”Lokacin ba ma wasan yake yi ba a’a yana bayar da horo ne a filin wasan aka ga ya yanke jiki ya fadi kasa”.An ce lafiyarsa kalau ya tafi garin Asaba saboda wasan ko da ya isa can sai da ya kira iyalansa ya shaida musu cewa ga shi ya isa lafiya .