Yankewar Kasuwanci Ya Sanya Mutane Yin Kaura A Yobe

0
395
Rabo Haladu Daga Kaduna
‘YAN kasuwa da al’ummar garin Buni Yadi da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe  sun bayyana rashin jin dadinsu bayan sojoji sun rufe daya daga cikin manyan kasuwannin garin.
Kasuwar Buni Yadi dai tana daya daga cikin manyan kasuwanni a jihar Yobe, kuma matakin rufe kasuwar ya janyo wasu na ficewa suna barin garin.
Mutanen garin sun ce sojojin sun rufe kasuwar ne tsawon wata guda abin da ya jefa al’umma da ‘yan kasuwar cikin takura da matsi ta yadda harkoki suka tsaya cak.
Sai dai rundunar sojin ta bakin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar Operation Lafiya Dole, shiyya ta biyu, Kyaftin Njoka Irabor ya ce kasuwar ta Buni Yadi kamar sauran kasuwanni ne da hukumomi suka rufe saboda matsalar tsaro.
Ya bayyana cewa idan har jami’an tsaro suka tabbatar da babu wata barazanar tsaro, za a bude kasuwar.
Ya ba da misali da kasuwar Geidam wadda aka rufe ta tsawon shekara kuma daga bisani aka bude ta.
Wasu mazauna Buni Yadi sun shaida wa manema labarai cewa rufe kasuwar ya tilasta ma su dole yin kaura daga garin.
“Na shirya, zan fita na bar garin, idan Allah ya sa garin ya yi kyau kuma kasuwar ta dawo, sai mu dawo saboda noma,” a cewar wani mazaunin Buni Yadi.
Wani Mazaunin garin kuma ya bayyana mamakin yadda za a rufe kasuwar maimakon ana samun zaman lafiya a garin.
“Sojoji suna cikin gari, kuma wane irin abu ne idan an ce gari har da barikin soja, wane tsoro ne kuma sojan Najeriya zai ji ya ce wani zai zo ya kawo tashin hankalin da har zai hana jama’a cin kasuwar garin.”
Alhaji Basala Gwani Mala Kasule, shugaban kasuwar Buni Yadi ya ce rufe kasuwar ya jefa mutane cikin kunci domin ba su da wajen da za su je su siya ko su siyar don ciyar da iyalansu.
Ya kuma tabbatar da batun tserewa da wasu daga cikin ‘yan kasuwar suke yi inda ya ce shugabannin leburori sun same shi kuma sun koka kan rashin aikin yi wanda ya jefa iyalansu cikin wani hali.
Akwai kasuwanni da dama da sojojin suka rufe a jihar Yobe ciki har da ta Kukareta wadda take rufe tsawon shekara guda saboda barazanar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here