Ganduje Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Sababbin Masarautu

0
316
Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNAN Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sa hannu kan dokar nan mai cike da ce-ce-ku-ce ta kirkiro karin masarautu hudu a jihar.
Gwamnan ya sanya hannu kan sabuwar dokar ne da ta kunshi kafa masarautun Bichi da Rano da Karaye da Gaya bayan da majalisar jihar ta kada kuri’ar amincewa a ranar Alhamis.
Hakan ya nuna yanzu Kano tana masarautu guda biyar a jihar. Kuma Gwamnatin Kano ta amince da dokar ne duk da umurnin kotu da ta dakatar da amincewa da kudirin.
Kirkirar masarautu a Kano dai ya janyo ce-ce-ku-ce a jihar da Najeriya gaba daya inda aka samu mabanbantan ra’ayoyi.
Wata sanarwa da daya daga cikin mashawartan Ganduje ta bangaren yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fitar ta lissafo kadan daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa:
Ya ce dokar ta kunshi bai wa Gwamna cikakkiyar damar nada Sarakuna da kuma masu nada Sarki wato Kingmakers.
Dole ne kowacce masarauta ta mika wa gwamnatin jiha kasafin kudinta domin amincewa a kan yadda za ta kashe kudin.
Gwamna na da ikon rage darajar kowane Sarki a Kano daga Sarki mai daraja ta daya zuwa mai daraja ta biyu ko ta uku ma, idan bukatar hakan ta kama.
Gwamna zai iya tsige Sarki idan har Sarkin ya kaurace wa zaman Majalisar Sarakunan Jihar Kano wadda za a kafa nan gaba, idan har ya yi hakan ba tare da wani dalili kwakkwara ba.
Sarakuna za su iya bai wa Gwamnatin jiha shawara amma sai sun nemi izinin Gwamnan.
Kowanne Sarki dole ne ya kiyaye yin abin da zai iya zubar da mutunci da martabar al’ummarsa a idon duniya.
A baya-bayan nan ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheikh Dahiru Bauci ya roki Gwamnan jihar Kanon da ya janye aniyarsa ta dawo da sababbin masarautun jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here