An Kai Wa Ministan Sufuri, Amaechi, Hari A Madrid

0
393

Daga Usman Nasidi.

WASU matasan kungiyar yakin neman Biyafara IPOB mazauna kasar waje sun kai wa tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan Sufurin Najeriya, Rotimi Chibuike Amaechi, hari a birnin Madrid, kasar Andalus.

Ministan da kansa ya bayyana cewa Allah ya kiyaye shi ba su citar da shi kafin jami’an ‘yan sanda suka ceto shi ba.

Ya tafi kasar Andalus halartar taron yakar canjin yanayi na duniya da ake gudanarwa a kasar.

Ya ce: “Wasu mintuna da suka wuce, wasu batattun ‘yan Najeriya sun kawo min hari a taron yakar canjin yanayin da na zo halarta a Madrid, kasar Sifen.

“Jami’an ‘yan sandan kasar Andalus sun kawar da su kafin su cutar da ni. Ina nan lafiya kuma ban samu rauni ba. Na gode da addu’o’inku da goyon baya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here