Ina Bukatar A Damko Wadanda Suka Kai Min Hari A Majalisar Dattijai – Hadiza Bala Usman

0
616

Daga Usman Nasidi.

MANAJAN daraktan hukumar jiragen ruwa ta Najeriya, Hadiza Bala Usman, ta yi kira da cewa a binciki wasu mutane da take zargi da hantararta a farfajiyar majalisar dattijai.

A koken da ta mika ga sufeta janar din ‘yan sanda, shugaban majalisar dattijai da kuma shugaban hukumar jami’an tsaro na fararen kaya, Hadiza Usman ta yi bayanin zuwan da ta yi majalisar don amsa gayyatar da aka yi mata a majalisar.

Ta bayyana cewa, wasu mutane sun hareta wadanda take zargin hayarsu aka yi. Ta zargi Idahosa Okunbo, shugaban OMSL da wannan lamarin.

“A yayin taron, Kaftin Idahosa na OMSL, bayan ya yi bayaninsa, ya fita daga taron a harzuke kuma da matukar fushi,” ta bayyana a kokenta.

Ta ce, “Bayan fitarsa, sai shugaban kwamitin hadin gwiwar da ya gayyace mu majalisar ya rufe taron. Bayan fita daga dakin taron, wasu ‘yan daba da suka rako Kaftin Idahosa sun biyo ni har kofar fita kuma sun yi kokarin su tarar da ni gaba da gaba. Sun zazzage ni cewa ina toshe musu da ubangidansu hanyar cin abinci kuma za su nemo ni tare da tarwatsa ni.”

Ta kara da cewa, kokarin jami’an tsaron da take tare da su ne tare da jami’an tsaron ofishin mataimakin shugaban majalisar dattijai ne ta samu fita tare da tawagarta ba tare da sun cimma burinsu ba.

Ta ce ya kamata a tuhumi Okunbo matukar wani abu mummuna ya faru da ita ko wani daga iyalinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here