Miyagu Sun Karbe Kasa Daga Hannunmu – A’isha Buhari

0
383

Daga Zubair A Sada Da Usman Nasidi.

UWARGIDAN shugaban kasar Najeriya Hajiya A’isha Buhari, ta ce ‘miyagun mutane’ sun karbe mulkin kasar daga hannun mutanen da ya dace su rika tafiyar da ragamar mulkin kasar kamar yadda The Cables ta ruwaito.

A’isha ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin hirar wayar tarho da aka yi da ita a wani shiri na Television Continental (TVC).

Ta ce bai dace wadanda ya kamata su rika tafiyar da gwamnati su yi shiru ba yayin da wasu mutane ke amfani da kafafen sada zumunta suna kokarin bata sunan gwamnati.

Ta ce labaran karya da ake wallafawa sun jefa ta cikin damuwa musamman lokacin da ake rade-radin cewa shugaban kasa ya mutu da kuma lokacin da aka ce shugaban zai kara aure.

“Ban dauke shi da muhimmanci ba saboda mijina ma bai san abin da ke faruwa ba,” ta ce game da rade-raden kara auren shugaban kasar.

“Dukkanmu ba mu san abin da ke faruwa ba; kawai sun fara yadda labarin ne a kafafen sada zumunta. Yanzu suna amfani da kafafen sada zumunta domin kawo karshen gwamnati.

“Ina tunanin bai dace mu kyale mutanen da ba su kai sun kawo ba su ci zalin ‘yan kasa nagari; Ban san dalilin da ya sa mutanen da ya dace su dauki mataki suka yi shiru ba yayin da bata-gari ke kwace kasar daga hannunmu. Ba zai yiwu ba kuma ba za mu amince da hakan ba.”

A’isha ta kuma ce hadiman shugaban kasa da sauran ma’aikatan gwamnati suna watsi da muhimman abubuwan da ya dace su dauki mataki a kai kana suna mayar da hankali kan abubuwan da bai shafi shugaban kasa ba.

Ta ce, “Duk lokacin da ya dace su (hadiman shugaban kasa) su dauki mataki kan masu aikata laifuka ko su gargade su sai su ja bakinsu su yi shiru.”

“Amma idan abubuwan da ba su da muhimmanci ne mutane za su fara magana kan shugaban kasa. Misali shi ne abin da ya faru bayan zaben Bayelsa. Lokacin da PDP ta fito ta ce za ta dakatar da tsohon shugaba, Goodluck Jonathan kan aikata wani laifi ko wani abu mai kama da haka.

“Ban ga dalilin da zai sa fadar shugaban kasa ta fito ta ce ta yi mamakin jin hakan ba. Matsalar su ne? Su ‘yan PDP ne? Shin Jonathan dan jam’iyyarmu ne? Mene ne hadin fadar shugaban kasa da lamarin?”

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here