2020: NAHCON Ta Bayyana Adadin Kejerun Aikin Hajji Da Saudiyya Za Ta Ba Najeriya

0
579

Daga Usman Nasidi.

HUKUMAR kula da ayyukan Hajji ta Najeriya, NAHCON, a ranar Asabar ta ce ta samu kujeru 95,000 na maniyyatan aikin Hajji na shekarar 2020.

Wannan na kunshe ne a takardar da shugabar bangaren hulda da jama’a ta hukumar NAHCON, Fatima Usara, ta ba manema labarai a garin Abuja.

Ta ce, an sa hannu a yarjejeniya tsakanin karamin ministan harkokin waje na Najeriya, Zubairu Dada da kuma ministan ayyukan Hajji da Umara, Saleh Benten.

Ta ce, an sa hannu a kan yarjejeniyar ne a ranar 5 ga watan Disamba, a shirye-shiryen aikin Hajji na 2020.

“A yayin saka hannun, Ambasada Dada ya mika godiyar Muhammadu Buhari ga Sarki Salman Bin Abdulaziz da kuma hukumomin ayyukan Hajji da suka biya diyyar mutane biyar da suka rasu tare da mutane shida daga Najeriya da suka yi hatsari a Makkah,” inji ta.

Kamar yadda ministar ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari na mika godiyarsa a kan karamci da goyon baya da mahajjatan Najeriya ke mora a kasar ta Saudi Arebiya.

Dada ya ce, shugaba Buhari ya kara da mika kokon barar bukatarsa ga hukumomin Saudi Arebiya da su ci gaba da ba da taimako ga NAHCON ta kowacce siga da ta shafi mahajjatan kasar nan.

Abdullahi Saleh, mukaddashin shugaban NAHCON kuma mukaddashin kwamishinan ayyuka na hukumar, ya bayyana godiyarsa ga ma’aikatar ayyukan Hajji da Umarah. Ya kara da kira gare su a kan hadin kansu da goyon bayansu a kowanne bangare.

Kamar yadda yarjejeniyar ta bayyana, “ mahajjata za su iya biyan riyal 100 ko sama da haka don ta zame musu inshorar hadurra, asarar dukiya da sauran hadurra da mahajjata kan iya fuskanta. Amma kuma hakan bai shafe kudin magani ba a kasar ta Saudi Arebiya.”

“A bayani a kan hatimin shiga kasar, wakilan sun yanke Riyal 300 na kowanne irin hatimi,” takardar ta ce. Takardar ta kara da cewa, hatimin bai shafe daga lokacin Umara ko ziyara ba zuwa lokacin Hajji.

Jakadan kasar Saudiyya din ya kara da jinjina wa kokarin NAHCON wajen hana take sharuddan hatimin shiga kasar tare da al’amuran da suka shafi aikin Hajji. Ya tabbatar wa da NAHCOn cewa, Saudi Arebiya za ta kara gina makewayi 60,000 don shawo kan matsalolin makewayi da ake fuskanta a yayin aikin Hajjin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here