Yarjejeniyar Samar Da Taki Tsakanin Najeriya Da Kasar  Moroko Kamfanin Taki 25 Suke Aiki

0
357
Rabo Haladu Daga Kaduna
 A wani yunkuri na ganin Najeriya ta samu wadatar Sinadarin inganta noma domin kasar ta ciyar da kanta, mahukunta  sun shiga wata yarjejeniya da kamfanin OCP na kasar Moroko.
Wannan yarjejeniya da Najeriya ta shiga da kamfanin OCP ta kasar Moroko tuni ta fara aiki wajen yin binciken irin kasar noma da manoman Najeriya ke amfani da ita domin gano irin takin zamanin da zai sa a samu amfanin gona mai yawa.
A yanzu haka, kamfanin OCP yana horar da ma’aikatan kamfanonin sarrafa takin zamani na Najeriya a babban birnin taraiyya Abuja, in ji babban jami’in OCP a Najeriya Caleb Usoh.
Wanda yayi bayanin cewa yarjejeniyar babba ce kuma tun shekara 2016 kamfanin ya fara aiki tare da manoman Najeriya.
A yanzu haka ana horar ma’aikata dabarun sarrafa takin zamani ta yadda manoma za su samu takin dayawa kuma iri daban daban har sai sun zaba kuma a kudi mai rahusa.
A cikin jami’an da aka horar akwai Mohammed Abubakar Maimalari, na kamfanin Excel Standard na kano da ya ce suna sarrafa taki buhu 1200 a rana.
Shi ma Emmanuel Fumen na kanfanin Tak Agro Fertilizers ya ce suna sarrafa taki 7,800 a rana kuma suna da ma’aikata na dindindin da na wucin gadi 270 a Funtua kawai.
Amma ga Augustine Akakpo na kamfanin Golden Fertilizers da ke Lagos, ya ce suna sarrafa ton dubu 70 a shekara.
A yanzu dai ana da kamfanonin sarrafa taki 25 a Najeriya wadanda sannu a hankali za su dauki ma’aikata dubu 75 a shekara daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here