Gwamna Ganduje Yana Cimma   Nasarori Wajen Aiwatar Da Manufofin Kiwon Lafiya -Dokta Nafi’u Tofa

0
373

Jabiru A Hassan, Daga  Kano.

WANI kwararren likita da ke jihar Kano, Dokta Nafi’u Yakubu Mohammed Tofa ya ce  gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje tana cimma kyawawan nasarori wajen aiwatar da manufofinta kan harkar kula da lafiya a matakai daban-daban.

Ya yi wannan tsokaci ne a zantawarsu da wakilinmu dangane da yadda gwamnatin jihar  Kano ta dauki karin jami’an lafiya 920 domin yin aiki a matakai daban-daban ta yadda za a ci gaba da samun nasarori wajen tafiyar da ayyuka da suka shafi kiwon lafiya.

Ya ce ko shakka babu fannin kula da lafiya yana samun goyon baya da tallafi daga  gwamnatin Ganduje wanda  hakan ta sanya  harkar lafiya ke tafiya cikin nasara, inda  kuma ya kara da cewa daukar karin ma’aikatan lafiya da Gwamna Ganduje ya yi zai taimaka wajen inganta  kula da lafiya ba tare da tsaiko ba.

Dokta Nafi’u Tofa ya kuma yi amfani da wannan dama  wajen isar da sakon fatan alheri ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kwamishinan lafiya Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa da dukkanin manyan jami’ai da ma’aikatan lafiya da kuma masu ruwa da tsaki kan harkar kula da lafiya saboda haduwa da aka yi ana aikin kiwon lafiyar al’umma ba tare da nuna  gajiyawa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here