Jami’ar Jos Ta Yi Bikin Yaye Dalibai 11,431  

0
340

Isah Ahmed Daga Jos

JAMI’AR Jos ta yaye dalibai guda 11,431 a bikin yaye dalibanta karo na 31 zuwa 32 da ta gudanar a karshen wannan makon, a garin Jos babban birnin Jihar Filato.

Da yake jawabi wajen bikin, mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Sabastian Maimako ya bayyana cewa wadannan dalibai da Jami’ar ta yaye. Sun hada da dalibai guda 3,385 da suka kammala a shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2017, da dalibai guda 3,638 da suka kammala a shekara ta 2017 zuwa shekara ta 2018 da kuma dalibai guda 2260, da suka kammala a  makarantu daban-daban da suka yi hadin gwiwa, da jami’ar.

Har’ila yau ya ce a wannan shekarar, jami’ar ta karrama wasu mahimman mutane guda biyu  da digirin girmamawa, saboda irin gudunmawar da suke bayarwa kan harkokin bunkasa ilmi da samar da ayyukan yi.

Ya ce wadannan mutane da jami’ar ta karrama sun hada da tsohon sakataren hukumar jami’o’i ta Najeriya [NUC], Farfesa Peter Okebukola da shugaban rukunan kamfanonin NASCO Mista Attia Nasreddin.

Mataimakin shugaban jami’ar ya godewa gwamnatin tarayya, da sauran masu ruwa da tsaki kan irin gudunmawar da suke bai wa jami’ar.

A nasa jawabin shugaban jami’ar Farfesa Toni Momoh ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan irin karfin gwiwar da yake bai wa gidauniyar tallafawa manyan makarantun kasar nan ta [TETFund].

Ya ce babu shakka irin ayyukan gine-ginen cibiyoyin bincike  da wannan gidauniya take yi a wannan jami’a, za su sanya ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan jami’o’in kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here