‘Yan Boko Haram Sun Yi Garkuwa Da Malamin Kwalejin Gashuwa

0
563
 Muhammad Sani Gazas Chinade, 
Dqga Damaturu
BIYO bayan kai wani harin da ake kyautata zaton maharan Boko Haram ne suka kai a garin Babban-Gida, shalkwatar karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe- da tsakiyar ranar Laraba makon jiya. Inda kuma mayakan suka yi awon gaba da malamin kwalejin ilimin jihar da ke Gashuwa: Umar Suleiman College of education, Mista Bitrus Zakka.
Wasu rahotanin da ba na jami’an tsaro ba a jihar, sun bayyana cewa an yi garkuwa da malamin a garin Babban-Gida, mai tazarar kilo mita 53 zuwa Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Bayanan sun ci gaba da shaidar da cewa an sace Mista Zakka a cikin motar haya, a lokacin da mayaqan suka tsayar dasu tare da umurtar kowane fasinja ya bayyana kan sa (ID Card), wanda ganin sa dauke da shaidar malantar ne, nan take suka bukaci ya sauka daga motar, inda nan take suka yi awon gaba da shi.
Wata majiya daga kwalejin, wadda ba ta yarda a bayyana sunanta ba, ta shaida wa wakilin mu cewa, wanda aka sacen, malami ne a sashen koyar da addinin kiristanci a makarantar.
A hannu guda kuma, mayaqan sun yi awon gaba da motar xaukar majinyata a wannan harin, wadda suka kwace daga hannun jami’an kiwon lafiya matakin farko a qaramar hukumar; a sa’ilin da ayarin jami’an suke kan hanya zuwa aikin riga-kafi, kusa da qauyen Muri- Mafa a karamar hukumar Tarmuwa.
Ma’aikatan masu gudanar da aikin riga- kafin, waxanda suka bar garin Babban-Gidan, shalkwatar qaramar hukumar Tarwuma, a kan hanyar su ta aiwatar da aikin riga-kafin, kafin maharan su farmake su tare da yin awon gaba da motar daukar majinyatan.
Duk kokarin da wakilin mu ya yi don jin ta bakin jami’an tsaro abin ya ci tura. Kuma har lokacin kammala wannan rahoton, babu wani cikakken bayani daga vangaren jami’an tsaro, balle kuma gwamnatin jihar Yobe.
 
Wakilinmu ya kokarin jin ta bakin shugabanin kwalejin ilimin jihar Yobe (Umar Suleiman College of Education) don samun karin bayani kan lamarin shima shiru. Yayin da wanni jigo a makarantar ya shaida wa wakilin cewa, ba za su iya cewa komai ba dangane da lamarin, ganin abu ne wanda ya shafi tsaro, kuma a kan hanya aka yi garkuwa da malamin, ba a makarantar ba. 
”Muna sauraron abinda jami’an tsaro za su ce kan wannan al’amarin. Amma ko ba komai muna cikin halin damuwa da abinda ya samu abokin aikin mu, kuma muna ci gaba da addu’ar Allah ya kubutar da shi a cikin qoshin lafiya”. In ji jami’in wanda bai yarda a bayyana sunan shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here