El-Rufai Na Daya Daga Cikin Mutanen Da Na Ji Dadin Aiki Da Su – Obasanjo

0
336

Daga Usman Nasidi.

TSOHON shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kwatanta Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da ‘dan baiwa’ kuma mutum mai kwazo na ajin farko da za a iya aiki da.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar ba zata da ya kai wa gwamnan a gidan gwamnatin jihar Kaduna a ranar Laraba.

Idan zamu tuna, Malam Nasir ya rike ministan birnin tarayya a yayin mulkin shugaban kasa Obasanjo.

Obasanjo ya kwatanta gwamnan da ‘dalibi nagari’, ya kuma kwakwayi watsi da banbancin jinsi ne a yayin mulkin Obasanjo.

“Yana daya daga cikin mutane nagari da na yi aiki da; El-Rufai dan baiwa ne,” Obasanjo yace.

“Muna da bukatar mutane irin shi. Mutumin da ka san yana tare da kai. Kuma zai iya duk aikin da ka saka shi.
“Ban ware mata a gwamnatina ba. Shima haka yayi a Kaduna. Dalibi ne nagari.”

Obasanjo ya kwatanta ziyararshi a matsayin komawa gida, saboda “shima dan jihar ne” . Ya bayyana cewa, ya gina gidanshi na farko a yankin Makera a tsakanin 1959 zuwa 1967 a lokacin da ya yi aiki a bataliyar Mogadishu ta sojin Najeriya a Kaduna.

Ya ce, wan nan bataliyar ce ta farko da ta kunshi ‘yan Najeriya daban-daban daga fadin kasar nan.

A mayar da martanin El-Rufai, ya kwatanta tsohon shugaban kasar a matsayin madubin dubawa. Ya kara da cewa, dabarun shugabancin da ya mallaka duk kwaikwayo ne daga madubin.

Ya mika godiya ga Obasanjo da ya samu lokacin kawo wannan ziyarar don ganin komai da idonshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here