Daga Shekarar 2023 Za Mu Daina Shigo Da Man Fetir – Shugaban NNPC

0
311

Z A Sada Da Usman Nasidi, Daga Kaduna

GWAMNATIN tarayya ta sanya shekarar 2023 a matsayin lokacin da za ta daina shigo da man fetir wanda aka tace daga kasashen waje gaba daya, domin tana sa ran zuwa lokacin matatun man fetirin Najeriya sun mike tsaye.

Shugaban hukumar man fetir ta Najeriya, Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin da yake rattafa hannu kan yarjejeniyar tsarin samar da kananan matatun mai a Najeriya da za su dinga samar da litan tataccen mai miliyan 20.

Kasar Najeriya dai ta dogara ne da tataccen man da ake shigo mata da shi daga kasashen waje wanda take sayar wa ‘yan kasa don amfanin yau da kullum sakamakon dukkanin matatun man kasar guda hudu sun daina aiki.

A jawabinsa, Mele Kyari, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damu matuka kan yadda Najeriya ta zamanto kasar da ta fi kowacce kasa sayan man fetir duk da cewa tana daga cikin kasashen da suka fi arzikin dan mai a duniya.

Sai dai ba wannan ba ne karo na farko da gwamnatin ta sanya ranar daina shigo da man fetir daga kasashen waje, domin kuwa a shekarar 2017 ma gwamnatin Buhari ta taba sanya shekarar 2019 a matsayin shekarar da za ta daina shigo da mai, amma sai ga shi kuma ta sake tsawaita lokacin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here