An Jinjina Wa Gwamna Masari Na Katsina

0
416

Mustapha Imrana Abdullahi

AL’UMMAR kauyen Yamadi da ke karamar hukumar Kankiya cikin yankin mazabar dan majalisar dattawa mai wakiltar Katsina ta tsakiya sun jinjina wa Gwamna Aminu Bello Masari bisa samar masu da na’ urar wutar lantarki mai karfin KVA 300.

Shi dai wannan kauye na Yamadi ya kasance babu wutar lantarki tsawon shekaru da dama saboda kamar yadda suka shaida wa manema labarai sun kasance a cikin matsalar rashin wuta tun shekaru 2015, don haka a yanzu suke godiya fa Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.

Kamar yadda mutane kauyen na Yamadi suka shaida wa kafar yada labarai ta rediyon vision cewa hakika wannan kokarin da Gwamna Masari ya yi masu ya sa sun tabbatar da kudirinsa na mai fadi da cikawa domin hakan zai kara bunkasa tattalin arzikinsu.

Mutane irinsu Magaji Nuhu, Sanusi Malam Garba, Abdul’azeez Karewa da Murtala Abdullahi Yamadi duk sun bayyana cikakken hadin kai da goyon bayansu ga Masari tare da gwamnatin da yake wa shugabanci bisa irin ayyukan raya kasa da yake wa jama’a, wanda ke tabbatar da samun ribar dimokuradiyya a fadin jihar baki daya.

Sun kuma yi godiya ga shugaban hukumar samar da hasken wutar lantarki na jihar Katsina Alhaji Abdullahi Bala Tanwa bisa irin yadda ya tabbatar da an kammala aikin cikin lokaci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here