Mustapha Imrana Abdullahi
HUKUMAR hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta tarayyar Nijeriya ta lalata miyagun kwayoyin Turamadol a wannan shekarar na naira tiriliyan daya.
Hukumar ta bayyana cewa sun samu nasarar kama wannan turamol ne a cikin sandukai da yawansu ya kai dari biyu da Hamsin (250) a cikin wannan shekarar a lakuta daban-daban.
In dai za a iya tunawa gwamnati a tarayyar Nijeriya ta haramta wannan kayan maye na turamol saboda irin yadda ake amfani da shi domin gusar da hankali.