”Mu Ba Wanzamai Mazauna Wuri Daya Ne Ba”

  0
  490

  Daga Z A Sada

  ALKAWARIN Allah ba ya tashi, kuma duk inda Allah ya kaddara mutum zai taka ko ya zauna ko kuma ayyukan hannu da zai yin a gado ne kokok haye ne sai mutum ya kai wannan matsayi, ko da ana mazuru ana shaho sai ya taka matsayin

  Wannan batu ne da ya fito daga bakin wadansu wanzamai guda biyu wadanda suke sana’arsu tare tamkar ‘yan biyu masu sunan Dauda Wanzami da Ahmad Wanzami da suka fito daga kasar Katsina amma an san su a garuruwa da dama kan wannan sana’arsu shekaru masuu yawan gaske

  ‘’Al’amarinmu ikon Allah ne kuma mu ba tallata kanmu muke yi ba, sannan ba tare da alfahari ba, aiki na wanzanci kowane iri bai da wahala ko kadan a wajenmu saboda horewar Allah SWT. Kuma wani abin ban sha’awa da Karin godiya babu wani day a taba cewa, ga sakamakon aikinmu daya da bai yi masa dadi ba’’. Inji su.

  Dangane da sana’arsu kuwa ta wanzanci suka ce, lokutan kaciya da ake yawan samun matsaloli a hannun wasu ‘yan na-iya ba ‘yan gado ba, su da sun sha yaro nan take suke umurtar iyayen da a ci gaba da sanya masa wando muddin za a kiyaye shawarwarin da suka bayar.

  Daga karshe suka yi nuni da cewa, lambobin wayarsu kawai suke bari a ggaruruwa da jihohin da suke zuwa a hannun matattarar mutane domin nemansu da sanin lokutan zuwansu. To, duk inda suka isa kira ne a waya babu kama hannun yaro. Suka ce ba su da wani abokin hamayya sannan suna yin abokantaka da mafi yawan ‘ya’yan da suke yi wa kaciya a sa- wando.

   

   

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here