An Fara Horar Da Malamai Dubu 32,000 A Jihar Katsina

0
510

Mustapha Imrana Abdullahi

A ci gaba da kokarin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari yake yi domin ganin harkar ilimi a dukkan fadin jihar ta kara bunkasa ya sa gwmanatinsa daukar wannan mataki na horar da malami.

Wannan aikin na horar da malamai dubu 32,000 ana yin sa ne tare da hadin gwiwar (Pleasant Library and book club) da gwamnatin jihar Katsina ta dauki nauyi domin ciyar da jihar gaba

Daukar nauyin ba da horon ya biyo bayan kokarin Gwamna Aminu Bello Masari na inganta harkar ilmi a jihar Katsina.

“PLBC ta dauki tsawon shekara biyar tana bada horo ga Malaman makarantun gwamnati a jihar Katsina kyauta, kafin gwamnati ta ba da umurnin horar da malamai baki daya na jihar Katsina”.

“Katsina State APC Social Media Crew ta ziyarci shiyyar Rimi da Mani wuraren da ake ba da horon. ranar Talatar da ta gabata 17/12/2019 aka kaddamar da shirin ba da horon”.

“A lokacin da muka ziyarci shiyyar karamar hukumar Rimi mun hadu da kwamishinan ilmi na jihar Katsina Furofesa  Badamasi Lawal Charanci da ya je duba yadda aikin ba da horon yake tafiya”.

“Mai girma kwamishinan ya yaba yadda aikin bada horon yake tafiya. Ya kuma ya yaba ma kokarin gwamnatin jihar Katsina karkashin Gwamna Masari na kula da inganta harkar ilmi a jihar Katsina”.

“A lokacin da kwamishinan ya kai ziyara a shiyyar ta Rimi ya samu tarba daga shugaban shirin ba da horon karkashin Kungiyar ta PLBC Dr Muktar na sashen koyon aikin jarida na makarantar kwalejin kimiyya da fasaha na Hassan Usman Katsina”.

“PLBC (Pleasant Library And Book Club) Engr. Muttaka Rabe Darma shi ne ya kirkiro da wannan tsarin suna kuma  daukar nauyin komi na tafiyar da shirin, don taimaka wa al’ummar jihar Katsina musamman bangaren ilmi”.

Aikin ba da horon zai  dauki wata daya ana yi, kuma ba da horon za a ba da shi rukuni-rukuni. Kowane rukuni za a ba shi horo na kwana uku kowane sati za a ba da horon har wata daya.

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here