Sarkin Kano Bai Gaisa Da Sababbin Sarakunan Kano Ba

0
275

Rabo Haladu Da Z A Sada Daga Kaduna

AN yi kallon-kallo tsakanin sarakunan jihar Kano a wurin taron yaye hafsohin ‘yan sanda da aka yi a garin Wudil na jihar Kano.

A wuin taron ne sarakunan jihar Kano guda biyar suka fara haduwa da juna tun bayan kafa sababbin masarautu hudu a jihar.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa wurin taron ne bayan sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye,wadanda hakimai ne a masarautar Kano kafin gwamnatin jihar ta nada su sarakunan yanka a sababbin masarautun da aka kirkiro a ‘yan watannin baya.

Sai dai sabbin sarakunan ba su gaisa da Sarki Sanusi ko sun yi magana da shi ko nuna sani ba.

Hakan ta sa aka yi mamaki, duba da dadaddiyar sanayyar da ke tsakaninsu da kasancewar dukkansu ‘yan majalisar masarautun jihar kuma manyan baki a wurin taron.

Sarki Sanusi ya iske sauran sarakunan zaune a kusa da juna, tawagarsa ta iske wani basarake daga babban birnin tarayya Abuja, zaune a kujerar Sarki Sunusi a wurin.

Sakamakon haka ne aka ware wa Sarkin wani wurin zama, abin da wasu ke gani a matsayin kaskantar da shugaban majalisar sarakunan jihar.

Bayan zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari taron, an sauya wa Sarki Sanusi wurin zama inda ya koma kusa da shugaban kasar a teburin da aka ware wa manyan bakin alfarma.

A karshen taron, shugaban kasa ya gaisa da Sarkin Kano Sunusi, amma sauran sarakunan ba su samu damar yin hakan ba, kasancewar Sarki Sunusi ne kadai a cikinsu yake sahun farko na manyan baki da ke kusa da shugaban kasa.

Taron shi ne karon farko da kwalejin horas da kananan hafsoshin ‘yan sanda da ke Wudil a jihar Kano ta yaye kananan hafsoshin ‘yan sanda mata.

A wurin bikin ne gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin habaka hazakar ‘yan sanda da kuma inganta kwalejin horas da hafsohin ‘yan sandan kasa da ke Wudil.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa ga sababbin hafsoshin su 620 da suka kammala karatu da horo ta fannin aikin dan sanda na tsawon shekara biyar.

Daga cikin sababbin hafsoshin, ASP Peter Joseph shi ne wanda ya fi hazaka, inda ya samu kyauta biyu a matsayin wanda da fi kokari ta fannin ilimi da kuma aikin dan sanda.

Buhari ya yi alkawarin inganta aikin dan sanda a kasar da kuma amfani da kwalejin wurin habaka kwazo da dabarun aikin dan sanda a kasa.

Shugaban ya kuma bukaci sababbin hafsoshin da su nuna kishin kasa a kodayaushe, kuma su yi amfani da abubuwan da suka koya wajen kare martabar Najeriya a idon duniya da ma cikin gida Najeriya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here