Gwamna Tambuwal Zai Gina Wa Hakiman Jiharsa Gidaje

0
274

Daga Usman Nasidi.

YAYIN da wasu ke bukatar a kwance wa sarkin gargajiyansu rawani, gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ta kaddamar da shirin gina wa Hakimai a jihar gidaje.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Aminu Abdullahi Abubakar, mai magana da yawun mataimakin Gwamnan, Mannir Muhammad Dan’iya, ya saki.

Mataimakin Gwamnan wanda shi ke jagorantan ma’aikatar kananan hukumomi ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugabannin rikon kwaryar kananan hukumomi 23 na jihar.

Mannir Muhammad ya bayyana cewa wasu daga cikin hakiman ba su da gidajen gudanar da ayyukansu saboda haka ya kamata a duba lamarinsu.

Bugu da kari ya bukaci shugabannin rikon kwaryar su kaddamar da sunayen makarantun firamaren kananan hukumominsu da ke bukatar gyara da talafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here