Matawalle Ya Kwace Kwangilar Naira Biliyan 76 A Zamfara

0
334

Daga Usman Nasidi.

GWAMNA Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya janye kwangilar Naira Biliyan 79.6 da aka ba kamfanoni daban-daban da suka hada da Alliance Trading Company, wanda mallakin Adamu Aliero ne, tsohon Gwamnan jihar Kebbi.

Kwangilar da ta kai darajar Naira Biliyan 25 da aka ba Alliance Trading Company Limited da wata mai darajar Naira Biliyan 27 da aka ba China Zhonghao a 2013 da 2018, duk Gwamna Matawalle ya kwace su a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar a ranar Laraba,18 ga watan Disamba, 2019.

Kwamishinan ayyukan jihar, Ibrahim Isa Mayana ya tabbatar da wannan ci gaban kuma ya sanarwa manema labarai. Ya ce an bukaci ‘yan kwangilar dasu dawo da kudaden ko su fuskanci fushin hukuma.

Ya kara da bayyana cewa, wasu daga cikin kwangilar da aka kwace ba a yi su yadda ya dace ba ko kuma an bar su ba tare da kammalawa ba ne, duk da ‘yan kwangilar sun amshe makuden kudaden.

Mayana ya ce:”An ba China Zhonghao kwangilar haka famfon burtsatse 84 a wasu karkara a kan Naira Biliyan 27.694 a 2018, kuma na biya su Naira Biliyan14.477. Amma sun bar kwanagilar bayan da suka kammala kashi 13 daga cikinta.”

“An ba kamfanin Alliance trading kwangilar N25.992bn don zagaye wasu yankunan karkara na kananan hukumomi 14 da wutar lantarki a 2013. A biya N22.599bn amma kamfanin ya bar kwangilar bayan da ya kammala kashi 67 a ciki.” cewar Mayana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here