Ba Ta Gamsu Da Yadda Ake Aikin Dam Na Ajiwa Ba – Mannir Yakubu

0
566

Mustapha Imrana Abdullahi

MATAIMAKIN Gwamnan jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu, ya bayyana  rashin gamsuwar gwamnatin  jihar karara a kan yadda ake gudanar da aikin gyaran Dam din Ajiwa.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakan lokacin da ya gana da manema labarai  lokacin da ya jagoranci wasu jami’an gwamnatin jihar a wata ziyara da suka kai sassan da aka ba da kwangilar tare da ma’aikatan kamfanin da ke gudanar da aikin.

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman a kan harkokin kafafen yada labarai na yanar Gizo Muhammad Barmo, Alhaji Mannir Yakubu ya bayyana cewa aikin wanda gwamnati ke kashe kimanin Naira Miliyan Dubu Biyu a kan shi, ya zuwa yanzu babu wani kokarin a zo a gani da kamfanin na KAIBO CONSTRUCTION ya yi.

Mataimakin Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatin za ta zauna da kamfanin don duba yiwuwar ba shi damar kammala aikin.

Daga cikin jami’an gwamnatin da suka mara wa mataimakin Gwamna baya sun hada da Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa, Kwamishinan Albarkatun Ruwa Alhaji Musa Adamu Funtua, Kwamishinan kuɗi Alhaji Kasim Umar Mutallab, Kwamishinan Shari’a Barista Ahmad Elmarzuq, Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri Alhaji Tasi’u Dahiru Dandagoro da sauran jama’a da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here