Daga Usman Nasidi.
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya amince da sababbin nade-nade a wasu hukumomi da ke karkashin ma’aikatar sadarwa ta kasa.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman a kafar sadarwa ta zamani da kafofin watsa labarai, Femi Adesina a wani jawabi ya bayyana cewa hakan na daga cikin manufar shugaban kasa na saurin cika kudirin ma’ikatar.
Wadanda aka nada su ne:-
Farfesa Adeolu Akande zai maye gurbin Sanata Olabiyi Durojaiye a matsayin shugaban kwamishinonin hukumar NCC.
Mista Uche Onwude zai maye gurbin Sanata Ifeanyi Godwin Ararume a matsayin Kwamishina daga yankin Kudu Maso Gabas.
Hukumar NITDA – Dakta Abubakar Sa’id da ya maye gurbin Farfesa Adeolu Akande a matsayin shugaba. Dakta Habibu Ahmed Imam (arewa maso yamma) wanda ya maye gurbin Dakta Lawal Bello Moriki da Dakta Mohammed Sa’idu Kumo a matsayin mamba na hukumar.
Hukumar aikawa da wasiku da sakonni (NIPOST) – An nada Dakta Ismail Adebayo Adewusi, shugaban hukumar inda ya maye gurbin Barrister Bisi Adegbuyi .
Hukumar Galaxy Backbone Limited (GBB) – An nada Farfesa Muhammed Bello Abubakar inda ya maye gurbin Architect Yusuf Kazaure.
Hukumar The Nigeria Communications Satellite Limited (NigComSat) – An nada Architect Yusuf Kazaure a matsayin shugaban kwamitin hukumar zai maye gurbin Cif Dakta George Nnadubem Moghalu.
Dakta Najeem Salam zai maye gurbin Honarabul Samson Osagie a matsayin Darektan kasuwanci da ci gaban hukumar.
Farfesa Abdu Ja’afaru Bambale zai maye gurbin Kazeem Kolawole Raji a matsayin Babban Darekta. Hadi Mohammed zai canji Mohammed Lema Abubakar a hukumar.