DSS Ta Kwace Wayoyin Salular Sowore Bayan Ta Sake Shi

0
405

Daga Usman Nasidi.

JAMI’AN hukumar tsaron sirri, DSS , ta sako tsohon dan takarar shugaban kasa, kuma fitaccen dan jaridar nan mai mallakin kamfanin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, sai dai ta hana shi wayoyin salularsa.

A ranar Talata, 24 ga watan Disamba ne hukumar ta saki Sowore bayan umarnin da babban lauyan gwamnatin Najeriya, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya bayar.

Sai dai duk da cika wannan umarni na ministan shari’a, hukumar DSS ta ci gaba da rike wayoyin salular Sowore, wanda hakan ke nuna suna kokarin sa idanu ne a kan sadarwarsa da kuma mu’amalarsa da mutane. Amma har yanzu hukumar bata da wani kwakkwaran dalilin yin hakan ba.

A ranar 3 ga watan Agustan 2019 ne hukumar DSS ta kama Sowore dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar AAC, inda ya samu kuri’u 30,000 kacal. Sai dai hukumar ta sake shi a ranar 5 ga watan Disamba, amma daga bisani ta sake kamashi a ranar 6 ga watan Disamba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here